Yadda kadarorin da Shugaba Buhari ya kwace daga barayi ke zurarewa - Inji wata hadimar sa

Yadda kadarorin da Shugaba Buhari ya kwace daga barayi ke zurarewa - Inji wata hadimar sa

Daya daga cikin masu baiwa shugaba Muhammadu Buhari shawara akan lamurran da suka shafi shari'a da kuma shirin sa na yin garambawula a harkar ayyukan shari'a Juliet Ibekaku-Nwagwu ta labarta yadda tace darajar wasu kadarorin da gwamnatin nan ke kwacewa suke ragewa.

A yayin da take fira da wakilin majiyar mu na Punch, Juliet Ibekaku-Nwagwu ta bayyana cewa rashin kyakkyawan yanayin aiki da kuma doka tsayayya suna cikin manyan matsalolin dake ci masu tuwa a kwarya.

Legit.ng ta samu haka zalika Juliet Ibekaku-Nwagwu ta bayyana cewa yanzu haka babu kyakkyawar dokar da ta ba gwamnati damar kula da kadarorin da kotu ta kwace daga hannun mutane a don haka ne ma wasu kadarorin ke lalacewa kuma darajar su na raguwa matuka.

A wani labarin kuma, Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun aika da sakon ban tsoro da razanarwa ga al'ummar garuruwa hudu a karamar hukumar Rabah ta jiha Sokoto dake da iyaka da jihar Zamfara inda suka sanar da su zuwan su a cikin 'yan kwanakin nan.

Majiyar mu ta Daily Nigerian dai ta bayyana cewa garuruwan da 'yan bindigar suka aikawa sakon sun hada da Ruwan Tsamiya da Kursa da Kaiwar Dawa da kuma Malela duk dai a karamar hukumar ta Raba.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel