Kasar China na duba yiyuwar soke dokar kayyade haihuwa

Kasar China na duba yiyuwar soke dokar kayyade haihuwa

- China na duba yiyuwar soke dokar kayyade haihuwa a kasar

- Dokar ta dauki tsawon shekaru 40 tana aiki a kasar

- A shekarar 2017, an haifi yara Miliyan 17.2 a kasar ta China

Rahotanni da muka samu na nuni da cewa, kasar Sin (China) na duba yiyuwar dage dokar nan da ta hana yin haihuwa barkatai a kasar, dokar da ta shafe shekaru akalla 40 tana aiki.

Rahoton da kamfanin dillancin labarai na Xinhua da ke kasar ya nuna cewa, babu inda aka ambaci shirin kayyade haihuwa a cikin sabon kundin tsarin kasar da ake sabuntawa, wanda aak turawa kwamitin zartaswa na kasar a ranar litinin.

Idan har an samu wannan canjin, to zai kawo karshen kayyade haihuwa, wanda tsawon shekaru 40 yayi sanadin rage yawan mutanen kasar, da kuma hadda banbancin jinsi da tilasta zubar da ciki, ko tara mai tsanani.

KARANTA WANNAN: Yadda amarya ta soke aurenta don mijin ya gaza tara kudin da zasuyi casu

Kadan daga cikin sabbin dokokin da aka gabatar, sun hada da dokar baiwa ma'aurata damar zama waje daya bayan sun rabu, don gujewa cin zarafin 'yancinsu. Ana sa ran kaddamar da wannan doka a shekara ta 2020.

A shekara ta 2016, gwamnatin China ta kawo karshe dokar haihuwar yaro daya, wacce take aiki tun 1979, inda aka amince da haihuwar yara biyu kawai.

Sai dai wannan canjin bai cika burin gwamnati na samar da karuwar mutane a kasar ba, domin kuwa an haifi yara Miliyan 17.9 ne a shekara ta 2016, inda ya sauka zuwa Miliyan 17.2 a shekara ta 2017.

Da yawa daga ma'aurata na tsoron haihuwar sama da yaro daya, saboda tsadar rainon yara a kasar, kasancewar da yawan matan kasar sun maida hankali wajen karo karatu, maimakon maida hankali wajen ayyukan gida da kula da yara.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel