‘Yan bingida sun hallaka mutane 2 ciki har da direban kakakin majalisar Filato

‘Yan bingida sun hallaka mutane 2 ciki har da direban kakakin majalisar Filato

- 'Yan bindiga sun yi tabargaza a garin Jos

- Sun kashe wani jami'in tsaro tare da Direban kakakin majalisar jihar

- Yanzu haka dai 'yan sanda sun bazama nemansu

Wasu ‘yan bindiga da ba’a san ko su wane ba sun kashe direban kakakin majalisar Filato Azi Magaji tare da wani jami'in asibitin koyarwa na Jami'ar Jos.

Kakakin hukumar ‘yan sanda na jihar Filato DSP Terna Tyopev, ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai (NAN) aukuwar lamarin a yau Lahadi.

‘Yan bingida sun hallaka mutane 2 ciki har da direban kakakin majalisar Filato

‘Yan bingida sun hallaka mutane 2 ciki har da direban kakakin majalisar Filato

Da yake shaidawa manema labarai, ya ce lamarin ya faru ne a yankin Zarazong dake karamar hukumar arewacin Jos.

"Jiya da misalin karfe 9:00pm na dare muka samu kiran waya, inda aka shaida mana wasu ‘yan bindiga sun suna harbi kan mai uwa da wabi a yankin Zarazong dake da dab da asibitn koyarwa na Jami'ar Jos, nan take muka tashi jami'an ‘yan sanda domin kai dauki ga jama'ar yankin." Kakakin ya shaida.

KU KARANTA: Zan kashe 'yan Boko Haram 1,000 idan na girma na zama soja - wani yaro mai shekaru 12

"Ko da zuwanmu sai muka iske gawar direban kakakin majalisa Mista Azi Magaji tare da wani jami'in tsaron asibitin koyarwa na Jami'ar Jos".

Daga nan ne kakakin hukumar ‘yan sandan ya tabbatarwa da jama'a cewa su kwantar da hankalinsu domin hukumarsu ta ‘yan sanda zata shawo kan matsalar.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel