Majalisar kasa zata zauna gobe, da yiwuwar ta rage kudin zabe da INEC ta nema

Majalisar kasa zata zauna gobe, da yiwuwar ta rage kudin zabe da INEC ta nema

- Biyo bayan yawaitar cece-kucen da ake yi kan kasafin kudin hukumar INEC, majalisa na shirin daukar mataki

- Majalisar kasar zata katse hutunta domin tsattsefe kasafin kudin gudanar da zaben

- INEC dai tana kan shan suka bisa dalilin bukatar kudin da ya wuce kima domin gudanar da zaben 2019

Zaman hadin gwiwar majalisun kasa zai dawo aiki daga gobe Litinin bayan katse hutunsu, yanke hutun dai ya biyo bayan aikin da za su yi kan kasafin kudin da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta gabatar a gaban zauren majalisar.

Majalisar kasa zata zauna gobe, da yiwuwar ta rage kudin gudanar da zabe da INEC ta nema

Majalisar kasa zata zauna gobe, da yiwuwar ta rage kudin gudanar da zabe da INEC ta nema

Hakan na kunshe ne cikin wani rahoto da wata majiya ta bayyana bayan kwamitin ya zauna da masu-ruwa-da-tsaki akan lamarin, sai wakilan kwamitin suka sake yin wani zaman a tsakanin su, inda suka amince da su sake haduwa a ranar da aka ayyana domin kammala aiki akan batun kasafin kudin.

Rahoton da jaridar PUNCH ta wallafa ya bayyana cewa, bayan kwamitin ya kammala aikinsa, zai mika sakamakon rahoton ne ga kwamitocin da suka dace na majalisar ta dattawa.

Rahoton ya kuma shaida cewa “Dalilin ci gaba da duba kasafin kudin da hukumar zabe ta kasa ta gabatar game da babban zaben 2019, wanda kwamitin hadin gwiwa na majalisar dattijai da majalisar wakilai ta kasa ke aiki a kansa, muna sanar da al’ummar kasa cewa, aikin akan hakan yayi nisa sosai kamar yadda shugabannin majalisun suka dora mana".

KU KARANTA: 2019: Abin da za a batar kan abinci ba zai wuce Biliyan 1 ba - INEC

Haka zalika kwamitin hadin gwiwar ya tattauna kan duk wasu mahimman abubuwa da suka shafi kasafin kudin, kwamitin kuma yana sane da hanzarin da ake bukata na zartar da kasafin kudin ta yadda za a iya yin aiki da shi a babban zaben 2019, hakan ya sanya wakilan kwamitin suke ta sadaukar da lokutan su, ba dare, ba-rana, domin su ga an kammala aikin akan lokaci.

Majalisar kasa zata zauna gobe, da yiwuwar ta rage kudin gudanar da zabe da INEC ta nema

Majalisar kasa zata zauna gobe, da yiwuwar ta rage kudin gudanar da zabe da INEC ta nema
Source: Depositphotos

Daga cikin kudaden da ake ganin majalisar zata zaftare sun kunshi; makudan kudin da aka ware har Naira biliyan N6b wajen ciyar da jami’an tsaro abinci da sauran wuraren da aka samu maimaici cikin kasafin kudin.

Ana sa ran zauren majalisar kasar zai yi muhawara akan kasafin kudin na hukumar zaben, wanda daga shi ne sai a mika shi inda za'a zartar da shi.

Tun da farko dai idan za'a iya tunawa dai Wakilan kwamitin suna ta ja-in-ja ne kan ko su amince da kasafin kudin na Naira biliyan 189 da hukumar zaben ta nema, ko kuma su amince da wanda shugaba Buhari ya mika musu na Naira bilyan 143, wanda shi ne ke cikin kasafin kudin shekarar 2018.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel