Jam’iyyar APGA za ta fidda dan takarar shugaban kasa daga Arewacin Najeriya

Jam’iyyar APGA za ta fidda dan takarar shugaban kasa daga Arewacin Najeriya

- Jam'iyyar APC ta samu koma baya kan jam'iyyun da zasu mara mata baya

- APGA zata tsayar da nata dan takarar shugabancin kasar nan a zaben 2019

Gabanin zaben shekarar 2019, kwamitin amintattu na jam’iyyar APGA sun bayyana cewa za su fitar da wanda zai yi mata takarar shugabancin kasar nan a zaben da yake matsowa.

Jam’iyyar APGA za ta fidda dan takarar shugaban kasa daga Arewacin Najeriya

Jam’iyyar APGA za ta fidda dan takarar shugaban kasa daga Arewacin Najeriya

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a birnin Akwa na jihar Anambara, inda ta cimma matsayar fitar da dan takarar shugabancin kasar nan daga shiyyar Arewa, yayin da kuma mataimakinsa zai fito ne daga shiyyar kudu maso gabashin kasar nan.

Sanarwar Bayan taron ta bayyana cewa an gudanar da taron wanda aka cimma wannan matsaya ne a gidan gwamnatin jihar Anambara, karkashin gwamnan jihar Willie Obiano wanda kuma shi ne jagoran jam’iyyar na kasa.

KU KARANTA: Ba na gudun a tsige ni daga Shugaban Majalisar Dattawa – Inji Saraki

Da yake wa manema labarai karin bayani babban sakataren kwamitin amintattun jam’iyarr Alh Sani Shinkafi, ya bayyana cewa “Bayan dukkanin tuntuba da muka yi, wanda muka yi amfani da rinjayen ra'ayin ‘yan jam’iyya, APGA ta cimma matsayar yin amfani da tsarin karba-karba, inda za ta fitar da dan takara daga yankin arewa tare da mataimakinsa daga bangaren kudu maso gabas".

Wata majiya a cikin jam’iyyar ta APGA ta bayyana cewa jam’iyyar tana muradin wani dan takara daga arewacin kasar nan, wanda ya kasance mai tasiri sosai.

“Dan takarar baya cikin jam’iyyar ta APGA yana cikin wata jam’iyyar daban, amma muna fatan zai dawo cikin jam’iyyar APGA matukar bai samu tikitin takara ba a cikin jam’iyyar da yake ciki yanzu ba".

A karshe majiyar ta bayyana cewa jam’iyyar ta APGA ta ajiye kudirinta na marawa shugaba Muhammad Buhari baya.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel