Atiku ya caccaki Shugaba Buhari a game da zuwa Landan ganin Likita

Atiku ya caccaki Shugaba Buhari a game da zuwa Landan ganin Likita

Mun samu labari cewa Jama’a da dama sun yi ca a kan tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar a dalilin wata magana da yayi a shafin sadarwa na zamani na Tuwita cikin ‘yan kwanakin nan.

Atiku ya caccaki Shugaba Buhari a game da zuwa Landan ganin Likita

Atiku yace Buhari yayi watsi da asibitocin gida ya maida hankali a waje

Atiku Abubakar wanda ya rike mukamin Mataimakin Shugaban kasar nan ya soki lamirin Shugaba Muhammadu Buhari na biyan kudin maganin wani Bawan Allah. Atiku ya yabawa Shugaban kasar amma yace Gwamnatin sa ta gaza.

Tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya nuna cewa da ace Gwamnatin Buhari tayi abin da ya dace a wajen harkar kiwon lafiya da ba haka ba. Atiku yace ina ma Buhari ya maida hankali wajen gyara asibitocin gida maimakon zuwa waje.

KU KARANTA: Yanzu mutane sun fahimci cewa Buhari garau yake - Fadar Shugaban kasa

Wannan magana da Wazirin na Adamawa yayi ne ta sa mutane da dama su ka rika tambayar ko shi karan-kan shi a Najeriya Likitoci ke duba sa. Kusan dai babu yaren da ba ayi amfani da shi wajen jin ko a ina Atiku Abubakar yake jinya ba.

Mutane dai sun hurowa ‘Dan siyasar wuta inda su kace shi da Iyalin sa kasar waje su ke zuwa idan ba su da lafiya. Atiku wanda yake harin kujerar Shugaban kasa ya soki Buhari na yawan zuwa sibiti a Landan ba tare da gyara na asibitocin nan gida ba.

Shugaba Buhari dai ya dauki nauyin yi wa wani Matashin ne da ke yi wa kasa hidima maganin cutar makanta da ke damun sa. Hakan na zuwa ne daf da zaben 2019 don haka wasu ke ganin cewa akwai burbushin siyasa a cikin wannan lamarin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel