Ba na gudun a tsige ni daga Shugaban Majalisar Dattawa – Inji Saraki

Ba na gudun a tsige ni daga Shugaban Majalisar Dattawa – Inji Saraki

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki yace sam ba ya jin dar-dar din a cire sa daga matsayin sa. Saraki ya bayyana wannan ne a Garin Asaba bayan ya gana da Gwaman Delta Ifeanyi Okowa a jiya.

Ba na gudun a tsige ni daga Shugaban Majalisar Dattawa – Inji Saraki

Saraki yace a bi doka idan ana neman cire sa daga kujerar sa

Bukola Saraki ya bayyana cewa ba don gudun a tsige sa daga kujerar sa bane Majalisa ta gaza dawowa bakin aiki. Shugaban Majalisar yace zai fi kyau masu neman tsige san su maida hankali wajen ganin jama’a sun amfana da romon damukaradiyya.

Bayan Shugaban Sanatocin Kasar ya gana da Gwamnan na Delta, yayi hira da ‘Yan jarida inda ya fada masu cewa ko a jikin sa maganar tsige shi ba ta damun sa. Bukola Saraki ya kuma yi karin haske game da babbalin dalilin sa na ficewa daga Jam’iyyar APC.

KU KARANTA: Wata Jam'iyya za ta tsaida 'Dan Arewa takara a 2019

Dr. Bukola Saraki ya bayyana cewa Jam’iyyar APC ta toyewa ‘Yan Najeriya hakkin damukaradiyya a cikin shekaru ukun da tayi a Gwamnati. Saraki yace babu kuma adalci a tafiyar don haka ya fice daga Jam’iyyar domin ba haka su ka yi tsammani ba.

Saraki yace babu wata barazana da za ayi masu wajen hana su aikin su na wakiltar jama’a da kuma kafa dokokin da za su taimaki al’umma. Saraki dai yana ganin idan har za a bi tsarin damukaradiyya wajen tube sa daga kujerar sa to ba shi da wata damuwa.

Ministan labarai na kasar nanAlhaji Lai Mohammed ya bayyana cewa Bukola Saraki bai taba goyon-bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba saboda ra’ayin karen-kan sa. Ministan yace Saraki ya rufe Majalisa ne saboda batun karashen kasafin kudin 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel