Ministan Buhari ya karyata Saraki bayan ya jero manyan ayyukan da ake yi a Kwara

Ministan Buhari ya karyata Saraki bayan ya jero manyan ayyukan da ake yi a Kwara

Mun ji cewa Gwamnatin Najeriya ta zayyano wasu manyan ayyukan da ta ke yi a Jihar Kwara inda nan ne Mahaifar Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki bayan yace Buhari yayi watsi da su a Gwamnati.

Ministan Buhari ya karyata Saraki bayan ya jero manyan ayyukan da ake yi a Kwara

Gwamnatin Buhari ta lissafo ayyukan da tayi a Jihar Bukola Saraki

A wata hira da Ministan yada labarai na Gwamnatin Tarayya watau Lai Mohammed yayi, ya karyata batun cewa Gwamnatin Buhari ba tayi aiki a Yankin da Shugaban Majalisar Dattawan kasar ya fito ba kamar yadda yake rayawa.

Ministan yace Bukola Saraki ya fadi haka ne kurum domin kokarin neman abin da zai fadawa jama’a bayan ya bar APC ya koma PDP. Lai yace daga cikin ayyukan da ake yi akwa gyaran titin Ilorin-Jebba-Mokwa zuwa Birnin Gwari.

KU KARANTA: Ban da shirin tsayawa takarar Gwamnan Kwara - Lai Mohammed

Lai ya kuma ce Gwamnatin nan na aikin titin Ilorin-Omu Aran-Egbe da kuma wani bangare na titin Jihar Kwara zuwa Kogi ta Ajase Ipo-Offa-Erinle har zuwa Jihar Osun. Har wa yau akwai kuma titin Garin Kishi zuwa cikin Kaiama.

Ba nan kadan abin dai ya tsaya ba inji Ministan inda yace ana gyaran gadan Ohan da Moro da ke kan hanyar Ilorin zuwa Igbeti. Sannan kuma Gwamnatin Buhari na buda hanyar Michael Imoudu-Gonmo/Afon a cikin babban Birnin Ilorin.

Sauran ayyukan da Gwamnatin nan ke yi sun hada da titin Afon-Aboto; da kuma hanyar Garin Share zuwa Patigi, sai kuma wata babbar hanya da Echi zuwa Shayangi har Koro. Ministan yace Saraki duk ya tabbatar da wannan a lokacin yana APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel