Shugaban Majalisa Saraki bai taba marawa Buhari baya ba - Lai Mohammed

Shugaban Majalisa Saraki bai taba marawa Buhari baya ba - Lai Mohammed

Mun ji labari cewa Ministan yada labarai na Gwamnatin Najeriya yayi kaca-kaca Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki wanda yace bai taba marawa tafiyar Shugaban kasa Buhari baya ba.

Shugaban Majalisa Saraki bai taba marawa Buhari baya ba - Lai Mohammed

Ministan labarai Lai Mohammed ya soki Bukola Saraki

Alhaji Lai Mohammed ya bayyana cewa Bukola Saraki bai taba goyon-bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba saboda ra’ayin karen-kan sa. Ministan ya kuma ce Saraki ya rufe Majalisa ne saboda batun karashen kasafin kudin 2019.

Lai wanda shi ne Ministan labarai da al’adu na Najeriya ya bayyana wannan ne a wata hira da yayi da Jaridar Vanguard inda yake cewa Majalisar Tarayya ba ta ba Gwamnatin Buhari goyon bayan da ya dace ba duk da Jam'iyyar APC ce ke da rinjaye.

KU KARANTA: Wani ‘Dan Majalisa ya nemi APC tayi wa mutane bayanin bashin da Buhari ya ci wa Najeriya

Ministan ya roki Saraki ya ajiye duk wani banbamci ya bude Majalisa domin yin abin da ya dace na amincewa da karashen kasafin kudin shekarar nan. Lai ya nuna cewa tun farkon Gwamnatin nan Saraki bai taba goyon bayan Shugaba Buhari ba.

Har wa yau, Lai ya bayyana cewa ba zai nemi Gwamna a Jihar Kwara ba sai dai abin da ya ke nema shi ne Jam'iyyar APC tayi karfi a Yankin. Saraki dai ya bar APC ya koma PDP inda yace Gwamnatin Buhari tayi watsi da su, Ministan ya karyata wannan.

Kwnaki kun ji cewa Bukola Saraki ya maidawa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu martani bayan tsohon Gwamnan Legas din ya zargi Saraki da harin kujerar Shugaba Buhari. Yanzu haka dai Bukola Saraki yace ba ya tsoron a tsige sa a Majalisar Dattawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel