2019: Saraki ya yi kus-kus da wani gwamna a kudancin Najeriya

2019: Saraki ya yi kus-kus da wani gwamna a kudancin Najeriya

- Sanata Bukola Saraki ya ziyarci gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta domin tattaunawa da shi kan wasu muhimman abubuwa

- Shugaban majalisa, Bukola Saraki ya ce ko dan baya damuwa kan makircin da ake shiryawa na tsige shi

- Ya kuma ce ba gaskiya bane wai majalisar bata son komawa aiki saboda tsoron tsige shi

A ranar Juma'a, shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya gana da gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa a fadar gwamnati da ke Asaba, babban birnin jihar Delta.

A jawabin da ya yi bayan taron, Saraki ya ce ko kadan baya damuwa da duk wata makirci da jam'iyyar APC ke shiryawa na kokarin tsige shi daga kujerersa na shugabancin majalisa saboda sauya sheka da ya yi zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.

2019: Saraki ya ziyarci wani amininsa a kudancin Najeriya

2019: Saraki ya ziyarci wani amininsa a kudancin Najeriya

Masu nazarin harkokin siyasa suna kyautata zaton ziyara ta Saraki ba zata rasa alaka da batun tsayawa takarar shugabancin a karkashin tutan jam'iyyar PDP ba.

DUBA WANNAN: 2019: Dan takarar PDP ya yi tsokaci kan farin jinin Buhari a arewa

"Gwamna Okowa yana daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar PDP masu muhimmanci, ina mtukar mutunta shi hakan yasa nazo in saurare shi kuma mu tattauna a kan wasu batutuwa," inji Saraki.

Saraki ya yaba da irin ayyukan cigaba da ya gani a jihar Delta cikin shekaru uku inda ya ce, "akwai cigaba sosai a fanin tattalin arziki tun shekaru uku da suka gabata, an samu cigaba sosai a jihar Delta dama irin wannan cigaba muke son gani a jihohin mu."

Wasu daga cikin Sanatocin da su ka yiwa Saraki rakiya sun hada da Sanata Dino Melaye da Sanata Peter Nwaoboshi.

Saraki kuma ya ce labarin da ake yadawa na cewa majalisar ta tafi hutun ne saboda tsoron tsige shi ba gaskiya bane.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel