2019: Jam'iyyar PDP ta sace gwuiwar Dino Melaye

2019: Jam'iyyar PDP ta sace gwuiwar Dino Melaye

Jam'iyyar PDP na mazabar Sanata Dino Melaye ta ce babu dan takarar da za ta bawa tikitin takarar ba tare da hamayya ba. Da alamu hakan ba zai yiwa Sanata Dino Melaye dadi ba saboda yana tsammanin yadda aka karbe shi hannun biyu-biyu bayan sauya sheka daga APC zuwa PDP zai samu wata gata na musamman ne.

Shugabanin da masu ruwa da tsaki a jam'iyyar PDP da ke yankin Kogi ta yamma sunce babu wani dan takara da za'a bawa tikitin takarar kai tsaye ba tare da an gudanar da zaben fitar da gwani ba a zaben shekarar 2019.

Jam'iyyar ta cimma wannan matsayar ne a wajen taron masu ruwa da tsaki da shugabanin jam'iyyar wanda akayi a mazabar Kogi ta yamma a gidan wani mamban kwamitin amintatu na jam'iyyar, Janar David Jemibewon mai murabus a ranar Juma'a.

2019: Jam'iyyar PDP ta sace gwuiwar Dino Melaye

2019: Jam'iyyar PDP ta sace gwuiwar Dino Melaye

Mahalarta taron sunce wannan matakin da suka dauke shine zai tabbatar da cewa an hana yin babakere ko afkuwar wani abu makamancin hakan da zai kawo rabuwan kawunna tsakanin mambobin jam'iyyar.

DUBA WANNAN: Riba da amfanin da ke cikin soyaya ko auren mace soja

Jam'iyyar ta tabbatar da dukkan sabbi da tsaffin 'ya'yan ta cewa za'ayi adalci wajen zaben fitar da gwanin ga dukkan masu sha'awar tsaya takarar.

Kazalika, jam'iyyar ta kuma shaidawa dukkan masu sha'awan takarar su tanadi kudadensu da za suyi amfani dashi wajen yakin neman zaben saboda jam'iyyar ba za ta yiwa kowa hidimar zabensa ba.

Wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyar da suka hallarci taron sun hada da Janar David Jemibewon, Cif Sam Akande, Sen. Tunde Ogbeha, Musa Ahmadu, Shola Akanmode, Chief Abiodun Ojo, Shola Ojo, Alh Hassan Salahu, Sam Abenemi, Mrs Margret Orebiyi, Bar. Kola Ojo da dukkan ciyamomin kananan hukumomi na jam'iyyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel