Ba kanta: Gwamnonin PDP sun juyawa daya daga cikinsu baya

Ba kanta: Gwamnonin PDP sun juyawa daya daga cikinsu baya

A jiya, Juma'a, ne gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, ya kaddamar da takarar sa ta sake son zama gwamna a karo na biyu.

Sai dai wani lamari da ya dauki hankali shine yadda gwamnoni biyu ne kacal daga cikin gwamnonin jam'iyyar PDP suka halarci kaddamar da takarar gwamna Emmanuel.

Gwamnonin jihohin Kuros Riba, Bayelsa, Delta, Enugu, Ekiti, Taraba da Gombe sun kauracewa zuwa taron kaddamar da takarar ba tare da gabatar da wani uzuri ko aika wakilci ba.

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, da takwaransa na jihar Abiya, Okezie Ikpeazu, ne kadai suka halarci taron kaddamar da takarar.

Ba kanta: Gwamnonin PDP sun juyawa daya daga cikinsu baya

Gwamna Udom Emmanuel

Kazalika shugaban PDP, Uche Secondus, bai halarci wurin taron ba. Sai dai mai bawa jam'iyyar PDP shawara a kan harkokin shari'a, Mista Emmanuel Enoldem, dan asalin jihar ta Akwa Ibom kuma mai kusanci da gwamna Emmanuel, ya bayyana cewar ya wakilci Secondus.

Honarabul Onofiok Luke, shugaban majalisar dokokin jihar Akwa Ibom anda kuma ya jagoranci taron kaddanar da takarar ya koka a kan yadda mambobin majalisar 12 ne kawai daga cikin 24 suka halarci taron.

DUBA WANNAN: 2019: Jam'iyyar APGA ta mika takarar shugaban kasa ga babban dan siyasa a arewa

Gwamna Emmanul na fuskantar guguwa mai karfin gaske dake barazanar tafiya da kujerarsa daga tsohon gwamnan jihar, Godswill Akpabio, wanda ya koma jam'iyyar APC cikin watan nan, Agusta.

Masu hasashen siysar jihar ta Akwa Ibom na ganin zai yi matukar wahala gwamna Emmanuel ya kai labari a zaben 2019 saboda karin iko da magoya da yake da su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel