Bashin da Buhari ya karbo cikin shekaru 3 ya zarce abin da PDP da ci tun 1999 – Ben Murray Bruce

Bashin da Buhari ya karbo cikin shekaru 3 ya zarce abin da PDP da ci tun 1999 – Ben Murray Bruce

Sanatan Yankin Bayelsa ta Gabas Ben Murray Bruce ya bayyana cewa Gwamnatin APC ta Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta karbowa Najeriya makukun bashi bayan hawan ta mulki shekaru 3 da su ka wuce.

Bashin da Buhari ya karbo cikin shekaru 3 ya zarce abin da PDP da ci tun 1999 – Ben Murray Bruce

Sanata Ben Murray Bruce ya soki cin bashin Gwamnatin APC

Sanata Ben Murray Bruce yayi kaca-kaca da Gwamnatin Jam’iyyar APC game da halin tattalin arzikin da Najeriya ta ke ciki. ‘Dan Majalisar yace Gwamnatin Buhari ta ci bashin da ya haura abin da PDP ta ci tun a shekarar 1999.

Ben Bruce yace babu wani kyawun tattalin arzikin da aka samu a Gwamnatin Buhari. Sanatan ya nemi Jam’iyyar APC mai mulki tayi wa mutanen kasar nan bayanin inda aka kashe bashin da Najeriya ta ci daga 2015 zuwa yau.

KU KARANTA: Wani mai shirin takara a 2019 ya hakura da zaben 2019

Barista Festus Keyamo wanda shi ne kakakin yakin neman zaben Buhari a 2019 yace abubuwa sun mike a Gwamnatin Buhari. Keyamo yace kafin hawan Buhari, Jihohi da dama ba su iya biyan albashi har sai da APC ta karbi mulki.

Idan ba ku manta ba kwanaki Gwamnatin Buhari tace Najeriya na iya biyan duk tarin bashin da ke kan ta. Hakan na zuwa ne bayan hankalin Hukumar I.M.F ya tashi kan Tiriliyoyin bashin da Najeriya ke ci a cikin ‘yan shekarun nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel