Fasinjoji na mutuwa saboda direbobi masu matsalar gani -FRSC

Fasinjoji na mutuwa saboda direbobi masu matsalar gani -FRSC

- Hukumar FRSC ta fara yiwa direbobi gwajin idanu kyauta a karamar hukumar Funtua, jihar Katsina.

- Hukumar ta alakanta yawaitar afkuwar hadura a kasar da tukin direbobi masu fama da lalurar idanu

- Ta yi kira ga kungiyoyin direbobi, da su tilasta mambobinsu yin gwajin lafiyar idanu

Hukumar kiyaye hadura da kula da lafiyar tituna ta kasa FRSC ta bayyana damuwarta, akan yawaitar afkuwar munanan hadurra a fadin kasar, tana mai alakanta hakan ga direbobin da ke tuki alhalin suna fama da lalurar idanuwa.

Shugaban rundunar FRSC reshen jihar Funtua, ACC JB Ako, shine ya bayyana hakan a lokacin da ya jagoranci sauran jami'an tsaro da kuma malaman lafiya, zuwa tasoshin motoci dake a fadin karamar hukumar, don duba lafiyar idanunsu.

ACC JB Ako, ya ce mafi akasarin direbobi basu damu da zuwa duba lafiyar idanuwansu ba, wanda hakan barazana ce ga rayuwar fasinjojin da suka dauka, duba da cewar ba zasu iya ganin nesa ko kusa ba, kamar yadda ya danganci matsalar da mutum ya ke da ita.

Ana samun munanan hadura daga direbobi masu matsalar Ido -FRSC

Hukumar kiyaye hadura na gwada lafiyar idanun direbobi

"Daga lokacin da fasinja ya shiga mota, to rayuwarsa da lafiyarsa sun rataya ne akan wuyan direban. Idan idanuwan direban nada matsala, karshe zai jefar da su cikin rami, ko yin karo da wata motar, wanda ka iya jawo sanadin salwantar rayuka," a cewar sa.

KARANTA WANNAN: Wani Mutum ya kashe kansa bayan ya sha Tabar Wiwi ta yi ma sa karo

Ana samun munanan hadura daga direbobi masu matsalar Ido -FRSC

Hukumar kiyaye hadura na duba lafiyar idanun direbobi

Dangane da wannan shiri na duba lafiyar idanuwan direbobi a karamar hukumar Funtua, kwamandan rundunar ya ce: "Mun samu hadin guiwar babban asibitin Funtua, inda suka bamu likitocin ido, da su ne muke zagayawa tasha tasha na mota, don duba lafiyar idanuwan direbobin, kuma wannan aikin kyauta ne.

"Idan mun samu direba da matsalar ido, mukan bashi shawarwari, wasu lokutan ma mukan basu gilashin da zasu rinka amfani da shi. Sanya gilashi ba wai zunubi bane, hanya ce ta magance yawaitar hadurra a kasar."

Fasinjoji na mutuwa saboda direbobi masu matsalar gani -FRSC

Fasinjoji na mutuwa saboda direbobi masu matsalar gani -FRSC

Daga karshe ACC Ako ya yi kira ga daukacin kungiyiyin direbobi dake a kasar, da su tilastawa mambobinsu yin gwajin lafiyar idanunsu, don kare rayuka da dukiyoyin jama'ar dake hawa motocin haya a kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel