Hukumar 'yan sanda ta gayyaci Fani Kayode saboda kalaman kin addini

Hukumar 'yan sanda ta gayyaci Fani Kayode saboda kalaman kin addini

- Hukumar 'yan sandan Najeriya ta bukaci tsohon ministan sufurin jirage, Femi Fani Kayode ya gurfana a gabanta domin amsa tambayoyi

- An bukaci Fani Kayode ya bayyana a ranar 28 ga watan Augusta bisa zarginsa da laifi wallafa rubuce-rubucen batanci

- Ana sa ran zai gurfanar gaban SP Usman Garba a ranar 28 ga watan Augusta shekarar 2018

Hukumar 'yan sandan Najeriya ta gayyaci tsohon ministan sufurin jiragen sama, Cif Femi Fani-Kayode ya gurfana gabanta bisa zarginsa ta makirci da wallafa rubutu da ka iya tayar da zaune tsaye.

A wasikar da aka aike masa mai lamba CR/3000/1GP.SEC/MU/T.G/ABJ Vol.54/226, hukumar yan sandan ta bukaci tsohon ministan ya gurafanar gaban SP Usman Garba kafin ko ranar 28 ga watan Augusta 2018 kamar yadda Punch ta wallafa.

'Yan sanda ta gayyaci Fani Kayode saboda kalaman kin addini

'Yan sanda ta gayyaci Fani Kayode saboda kalaman kin addini

DUBA WANNAN: Sauyin sheka da harigido bai isa ya rikita ni ba - Shugaba Buhari

Wasikar wanda kwamishinan 'yan sanda mai kula da sanya idanu a hedkwatan 'yan sanda, Habu Sani, ya sanya hannu a kai ta ce rubutun da Fani Kayode ya wallafa tana tayar da hankulan jama'a.

A baya, Legit.ng ta ruwaito cewa Fani-Kayode ya musanta cewa ya fadi kalaman batanci a kan jam'iyyar PDP da wasu jiga-jigan jam'iyyar.

Fani-Kayode ya ce bashi ne ya wallafa rubutun da aka alakantawa da shi ba a wata sako da ya aikewa Legit.ng a ranar 10 ga watan Augustan shekarar 2018.

A cewarsa, jam'iyyar All Progressive Congress (APC) ce ke kokarin bata masa suna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel