An sanya Dokar taƙaita Zirga-Zirga a jihar Kaduna

An sanya Dokar taƙaita Zirga-Zirga a jihar Kaduna

Mun samu cewa, gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga gami da ƙuntatawa daga ƙarfe 7:00 na yammaci zuwa 7:00 na safiya a unguwanin Kwaru da kuma Yero dake karamar hukumar Kaduna ta Arewa tun a ranar Juma'ar da ta gabata.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, gwamnatin ta sanya wannan doka sakamakon kisan wasu matasa biyu yayin aukuwar wani rikici a tsakanin unguwannin biyu.

Kakakin fadar gwamnatin jihar, Samuel Aruwan, shine ya bayar da wannan sanarwa yayin ganawa da manema labarai na kamfanin dillancin labarai na kasa a jihar ta Kaduna.

Cikin sanarwar Aruwan ya bayyana cewa, jami'an tsaro na hukumomin daban-daban sun yawaita a unguwannin biyu domin tabbatar da tsaro gami da kwantar da tarzoma tare da dabbaka wannan doka ta ƙuntatawa.

An sanya Dokar taƙaita Zirga-Zirga a jihar Kaduna

An sanya Dokar taƙaita Zirga-Zirga a jihar Kaduna

A yayin haka gwamnan jihar, Mallam Nasir El-Rufa'i, ya jajantawa 'yan uwan wannan Matasa da ajali ya katse ma su hanzari tare da bayyana damuwar dangane da aukuwar wannan mummunan lamari mai tattare da baƙin ciki.

KARANTA KUMA: Najeriya za ta karɓi baƙuncin Shugabar 'Kasar Jamus, Merkel a ranar Juma'a

Kazalika gwamnan ya bayar da tabbacin sa ga 'yan uwan wadanda suka riga mu gidan gaskiya kan cewa, ya bayar da umarni ga hukumomin tsaror kan tsananta bincike domin cafko masu hannu cikin wannan mummunan ta'addanci

Legit.ng ta fahimci cewa, gwamnan ya kuma mika kokon barar sa gami da gargadin al'ummar unguwannin biyu kan zama lafiya da kuma kwanciyar hankali.

Rahotanni sun bayyana cewa, tawagar gwamnan da suka kai ziyara unguwannin biyu ta hadar da mataimakin sa, Mista Barnabas da kuma kusoshin gwamnati na jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel