Dalilin da yasa nayi tafiyar mita 800 a ranar Sallah – Shugaba Buhari

Dalilin da yasa nayi tafiyar mita 800 a ranar Sallah – Shugaba Buhari

- Shugaba Buhari ya bayyana cewa tafiya mai tsawo da yayi a ranar Sallah ba wai domin gwada lafiyar jikinsa bane

- Ya ce yayi shine domin mutunta dubban mutanen da suke so gaishe shi a wannan rana

- A cewar Buhari ya dade da nunawa yan Najeriya kuddirinsa na son takara

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa tafiya mai tsawo da yayi a ranar Sallah ba wai domin gwada lafiyar jikinsa bane sai dai yayi shine domin mutunta dubban mutanen da suke so gaishe shi a wannan rana.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakunci wasu kungiyoyin jama’a da suka ziyarce shi daga masarautar Daura a gidansa dake Daura, jihar Katsina a ranar Juma’a.

Dalilin da yasa nayi tafiyar mita 800 a ranar Sallah – Shugaba Buhari

Dalilin da yasa nayi tafiyar mita 800 a ranar Sallah – Shugaba Buhari

Shugaba Buhari yace ko daya takarwa bashi da nasaba da kudirinsa na sake takara a 2019, inda ya kara da cewa tuni ya dade da sanar da yan Najeriya game da kudirinsa na sake takara.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban Buhari ya bayyana cewa nasarorin da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta samu a zabukan cike gurbi a Katsina, Bauchi da Kogi sun nuna cewa jam’iyyar ce zata lashe zabe a 2019.

KU KARANTA KUMA: Zaben fidda gwani: Buhari zai san makomarsa a APC a ranar 19 ga watan Satumba

Buhari ya bayyana hakan yayinda ya karbi bakuncin wakilan shugabanni 34 na kungiyar kananan hukumomin Najeriya a jihar Katsina.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel