Nasarorin da jam’iyyarmu ta samu a baya-bayan nan ya nuna cewa zamuyi nasara a 2019 - Buhari

Nasarorin da jam’iyyarmu ta samu a baya-bayan nan ya nuna cewa zamuyi nasara a 2019 - Buhari

- Shugaba Buhari yace jam'iyyar APC ce zata lashe zabukan 2019

- Ya ce zabukan cike gurbi da akayi kwanan nan alamu ne dake nuni ga hakan

- Yayi alkawarin ci gaba da iya bakin kokarinsa wajen ganin ci gaban Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya ya bayyana cewa nasarorin da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta samu a zabukan cike gurbi a Katsina, Bauchi da Kogi sun nuna cewa jam’iyyar ce zata lashe zabe a 2019.

Buhari ya bayyana hakan yayinda ya karbi bakuncin wakilan shugabanni 34 na kungiyar kananan hukumomin Najeriya a jihar Katsina.

Nasarorin da jam’iyyarmu ta samu a baya-bayan nan ya nuna cewa zamuyi nasara a 2019 - Buhari

Nasarorin da jam’iyyarmu ta samu a baya-bayan nan ya nuna cewa zamuyi nasara a 2019 - Buhari
Source: Depositphotos

Ya mayar da hankali sosai a nasaroron zabukan baya-bayan nan cewa tabbass alamu ne na abubuwa masu zuwa.

Ya godema shugabannin kungiyar kan ziyarar Sallah da suka kai masa tare da sakon taya murna akan kokarin jam’iyyar da gwamnatinsa, ya basu tabbacin cewa zai ci gaba da yin iya bakin kokarinsa ga kasar.

KU KARANTA KUMA: Zaben fidda gwani: Buhari zai san makomarsa a APC a ranar 19 ga watan Satumba

Da yake magana a madadin mambobin kungiyar shugaban ALGON a jihar, Alhaji Mohammed Na’Allah ya nuna goyon bayansu da jajircewarsu wajen ganin nasarar gwamnatin Buhari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel