2019: Rikicin tikitin takarar shugabancin kasa ya raba kan masu ruwa da tsaki a PDP

2019: Rikicin tikitin takarar shugabancin kasa ya raba kan masu ruwa da tsaki a PDP

- Sauyan sheka da wasu 'yan siyasa su kayi daga APC zuwa PDP ya jefa jam'iyyar cikin tsaka mai wuya wajen zaben dan takarar shugabancin kasa a zaben 2019

- Tsaffin mambobin jam'iyyar PDP suna jin haushin yadda jam'iyyar ke fifita wadanda suka dawo jam'iyyar kwana-kwanan nan

- Magoya bayan Ekweremadu da Okechukwu suna sa-in-sa game da kujarar sanata na yankin Enugu ta yamma

Rahottanin da Legit.ng ta samu na nuna cewa kawunnan masu ruwa da tsaki da gwamnonin jam'iyyar PDP ya rabu a kan batun tsayar dan takarar shugabancin kasa a babban zaben shekarar 2019 mai zuwa.

New Telegrah ta ruwaito cewa rashin jituwan da ke tsakanin 'yan jam'iyyar ta PDP ya sake rinchabewa ne saboda sauya shekar da wasu 'yan jam'iyyar APC su kayi zuwa jam'iyyar PDP kwana-kwanan nan.

2019: Rikicin tikitin takarar shugabancin kasa ya raba kan masu ruwa da tsaki a PDP

2019: Rikicin tikitin takarar shugabancin kasa ya raba kan masu ruwa da tsaki a PDP

Jaridar ta ce kawunansu ya rabu ne tsakanin wadanda ke son a bayar da tikitin takarar ga wani cikin sabbin mambobin da suka shigo jam'iyyar da kuma wadanda ke ganin tsaffin mambobin da suka kasance a jam'iyyar tun 2015 ya dace a bawa tikitin takarar.

DUBA WANNAN: Sauyin sheka da harigido bai isa ya rikita ni ba - Shugaba Buhari

A halin yanzu akwai mutane 11 da ke sha'awar takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar ta PDP kuma dukkansu daga yankin Arewa suke. 'Yan takarar da aka ambato sun hada da:

1. Toshon mataimakin shugaban kasa Atiku, Atiku Abubakar

2. Tsohon gwaman jihar Jigawa , Sule Lamido

3. Tsohon ministan ayyuka na musamman, Kabiru Turaki

4. Tsohon shugaban rikon jam'iyyar PDP, Ahmed Makarfi

5. Senata Datti Baba Ahmed

6. Gwaman jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo

7. Tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau

8. Tsohon gwamnan Sakkwato, Attahiru Bafarawa

9. Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki

10. Gwaman jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal

11. Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso

Wata majiya daga hedkwatar jam'iyyar ta sanar da majiyar Legit.ng cewa tsaffin mambobin jam'iyyar kamar Makarfi da Lamido da sauransu basu jin dadin yadda jam'iyyar ke fifita wadanda suka sauya sheka daga APC.

Wata majiya ta ce wadanda suka tsaya a jam'iyyar tun shekarar 2015 suna ganin cikinsu ya dace a bawa wani tikitin takakarar saboda irin saduakarwar da suka yiwa jam'iyya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel