Yadda ganawa ta da Shugaba Buhari ta kasance a garin Daura - Shehu Sani

Yadda ganawa ta da Shugaba Buhari ta kasance a garin Daura - Shehu Sani

Da sanadin shafin jaridar Daily Nigerian mun samu cewa, a ranar Alhamis din da ta gabata ne Sanata Shehu Sani, ya kai ziyarar gaisuwa ta bikin babbar Sallah ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a Mahaifar sa ta garin Daura dake jihar Katsina.

Sanatan mai wakilcin jihar Kaduna ta Tsakiya, ya kuma mika godiyar sa ga shugaban kasar dangane da ruwa da tsakin da ya yi cikin rikita-rikita da kuma hargitsi dake fuskantar jam'iyyar ta APC reshen jihar Kaduna.

Sanata Shehu ya bayyana hakan ne yayin ganawar sa da manema labarai jim kadan bayan ganawar su ta bayan labule da shugaban kasar gidan sa na Daura dake Birnin Dikko.

Legit.ng ta fahimci cewa, shugabannin sun tattauna shawarwari kan al'amurran da suka shafi karfafa jam'iyyar ta hanyar warware matsalolin da ta ke fuskanta a halin yanzu kamar yadda Sanatan ya bayyana.

Yadda ganawa ta Shugaba Buhari ta kasance a garin Daura - Shehu Sani

Yadda ganawa ta Shugaba Buhari ta kasance a garin Daura - Shehu Sani

A cewar sa, ya kuma yi amfani da wannan dama ta jaddawa shugaban kasar goyon bayan mazabarsa wajen kada masa kuri'u karo na biyu a zaben 2019.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Aisha Buhari ta ƙaddamar da Cibiyar tallafawa Mata a Garin Daura

Sanatan ya kuma bayyana cewa, bai yanke shawarar ci gaba da kasancewa a jam'iyyar APC ba sakamakon sulhuntawa da fustattun shugabannin jam'iyyar reshen jihar sa ta Kaduna, sai dai ya yanke wannan hukunci sakamakon ruwa da tsakin shugaba Buhari da kuma shugabancin jam'iyyar na kasa baki daya.

A sanadiyar haka ya sanya Sanatan yake kira gami da mika kokon barar sa ga fusatattun mambobin jam'iyyar dake majalisar dokoki na tarayya, akan su kawar da duk wani bambance-bambance wajen hada kai da juna domin ci gaban jam'iyyar da kuma kasa baki daya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel