Dalilin da yasa na kashe basaraken Ekiti – Mai laifi

Dalilin da yasa na kashe basaraken Ekiti – Mai laifi

Mai laifin da ake zargi da dabama wani basaraken Odo Oro Ekiti, Oba Gbedabo Ogunsakin wuka har lahira ya amsa laifinsa a ranar Juma’a, cewa ya aikata laifin ne domin ya maye gurbin sarautar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa Omonoyi Ademola, wanda aka ce baida cikakken lafiya kafin ya aikata laifin yace shi bai san cewa Oban zai mutu ba.

Omoniyi, wanda ya kasance da mumunan kama ya bay an jarida mamaki da yadda yake turanci lokacin da kwamishinan yan sandan jihar, Mista Bello Muhammed ya gurfanar da su tare da wasu mutane 26.

Dalilin da yasa na kashe basaraken Ekiti – Mai laifi

Dalilin da yasa na kashe basaraken Ekiti – Mai laifi

Yayi ikirarin cewa marigayi sarkin ne ya fara kai masa hari lokacin da ya ziyarci fadarsa domin fada masa wani bayani mai muhimmanci.

Ya bayyana cewa ruhanai day an uwansu sun fada masa cewa sarautar ya zagayo kansa, don haka ya tafi fadar a wannan rana.

Sai dai a cewarsa bai je da niyar kashe sarkin ba.

KU KARANTA KUMA: Zaben fidda gwani: Buhari zai san makomarsa a APC a ranar 19 ga watan Satumba

Yace a lokacin da sarkin yaji abunda ke tafe da shi sai ya kai masa hari, shi kuma bai san cewa sarkin ai mutu ba idan ya rama.

Sai dai kwamishinan yan sandan yace bai gamsu cewa Omoniyi mahaukaci bane duba ga abunda ya aikata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel