'Yan sanda sun kashe 'yan fashi 4 da suka kai farmaki kusa da gidan Akpabio

'Yan sanda sun kashe 'yan fashi 4 da suka kai farmaki kusa da gidan Akpabio

- 'Yan sanda sun tabatar da kashe wasu 'yan fashi da makami guda hudu a garin Akwa Ibom bayan sunyi musayar wuta

- Da farko anyi ikirarin cewa 'yan fashin sunyi niyyar zuwa gidan Sanata Godswill Akpabio ne amma daga bayan 'yan sanda sunce ba haka lamarin ya ke ba

- 'Yan sanda sun far ma 'yan fashin ne yayin da suke amshe kudaden mutane a gaban wani banki da rana tsaka

Hukumar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Akwa Ibom ta sanar da cewa jami'anta sun kashe hudu daga cikin wasu da aka zargin 'yan fashi da makami ne da su kayi fashi a gidan man fetur da ke Ikot Ekpene a jihar Akwa Ibom a ranar 21 ga watan Augusta.

Fashin da a kayi a ranar 21 ga watan Augusta ya faru ne kusa da gidan Sanata Godswill Akpabio da ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC cikin 'yan kwana-kwanan nan. Hadimin Sanata Akpabio ya yi ikirarin cewa 'yan fashin sunyi niyyar zuwa gidan Sanatan ne amma 'yan sanda suka fatatake su.

'Yan sanda sun kashe 'yan fashi da makami hudu da suka kai farmaki gidan Akpabio

'Yan sanda sun kashe 'yan fashi da makami hudu da suka kai farmaki gidan Akpabio

DUBA WANNAN: Sauyin sheka da harigido bai isa ya rikita ni ba - Shugaba Buhari

Sai dai daga baya, hukumar 'yan sanda ta karyata zancen idan ta ce anyi fashin ne a wata gidan mai misalin kilomita 200 daga gidan tsohon gwamnan na jihar Akwa Ibom.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Adeyemi Ogunjemilusi ne ya bayar da sanarwan kashe 'yan fashin a wata taron manema labarai da ya kira a Uyo a ranar Juma'a.

Ya ce an kashe mutane hudu yayin da 'yan sanda ke musayar wuta da 'yan fashin sannan an kama guda cikinsu bayan an raunata shi da harsashi.

Mr Ogunjemilusi ya ce an kashe 'yan fashin ne yayin da suke fashi a wata banki da ke Ikot Ekpene inda suke kwace kudaden mutane a gaban na'urar cire kudi ta ATM da tsakar rana.

Kakakin hukumar 'yan sandan ya ce 'yan fashin suna fakewa da sana'ar achaba ne suna amfani da babur wajen aikata fashin, hakan yasa 'yan sandan jihar suka saka takunkumi a kan 'yan achaban har zuwa lokacin da suka zakulo bata gari cikin mambobinsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel