Zaben fidda gwani: Buhari zai san makomarsa a APC a ranar 19 ga watan Satumba

Zaben fidda gwani: Buhari zai san makomarsa a APC a ranar 19 ga watan Satumba

- Jam'iyyar APC zata gabatar da zaben fidda gwanayeta a watan Satumba

- Za'a gabatar dana shugaban kasa a ranar 19 ga watan Satumba

- Shugaba Buhari ya nuna ra'ayin sake takara a karo na biyu

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta sanya ranar Laraba, 19 ga watan Satumba a matsayin ranar zabar dan takarar kujerar shugaban kasar ta.

Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna ra’ayinsa na takarar kujerar shugabancin kasar karo na biyu kuma ana sanya ran shi zai dauki tikitin jam’iyyar.

Zaben fidda gwani: Buhari zai san makomarsa a APC a ranar 19 ga watan Satumba

Zaben fidda gwani: Buhari zai san makomarsa a APC a ranar 19 ga watan Satumba

Shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole a wata wasika mai kwanar wata 17 ga watan Agusta zuwa ga shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Mahmood Yakubu yace jam’iyyar na bukatar gabatar da taron kasa domin zabar tawagar ta a ranar Asabar, 8 ga watan Satumba.

KU KARANTA KUMA: Makiyaya na shirin kashe ni - Ortom

Haka jam’iyyar ta bukaci gabatar da taron fidda gwani na gwamna a ranar 24 ga watan Satumba. Na majalisar dattawa a ranar 20 ga watan Satumba, majalisar wakilai kuma ranar 19 ga watan Satumba, sannan na majalisar dokokin kasa a ranar 29 ga watan Satumba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel