Jama’a su na huro mani wuta in nemi takarar Sanata – Chris Ngige

Jama’a su na huro mani wuta in nemi takarar Sanata – Chris Ngige

Mun samu labari cewa Ministan kwadago na Gwamnatin Buhari Sanata Chris Ngige ya bayyana cewa an matsa masa lamba ya fito takarar ‘Dan Majalisar Dattawa a zabe mai zuwa domin akwai bukatar wadanda su ka san aiki.

Jama’a su na huro mani wuta in nemi takarar Sanata – Chris Ngige

Sanata Chris Ngige na neman komawa Majalisar Dattawa a 2019

Chris Ngige yake cewa mutanen sa sun huro masa wuta ya nemi kujerar Sanata kuma yana tunanin ya tsaya takarar. A lokacin da Ngige yake jawabi a Garin Obosi da ke cikin Karamar Hukumar Idemili yace yana shawarar tsaya takara.

Dr. Chris Ngige na tunanin sake komawa Majalisar Dattawa a zaben 2019. Ministan yace nan da makonni biyu zai bayyanawa Duniya matsayar sa. Daga cikin masu matsawa Ministan yayi takara a 2019 akwai mutanen Mazabar sa.

KU KARANTA: Shugaba Buhari na zuba ayyuka kusan 100 a Kudancin Najeriya

Daga cikin dalilan da Ministan ya bada na komawa Majalisar Kasar shi ne ganin sa-in-sar da ake samu tsakanin ‘Yan Majalisa da kuma Shugaban kasa. Ngige yace don haka ne ake tunani ya kamata irin su ne za su wakilci Talakawa a 2019.

Sanata Ngige yayi Gwamnan Jihar Anambra tsakanin 2003 zuwa 2006 inda bayan nan kuma ya wakilci Anambra ta tsakiya daga 2011 zuwa 2015. A 2015 ne Shugaban Kasa Buhari ya nada Ngige a matsayin Ministan kwadagon Najeriya.

Kwanaki kun ji cewa Ministan kwadagon yayi magana game da albashin Ma’aikata a Najeriya inda yace Shugaban kasa Buhari ya damu da halin jama’a don haka ake tunanin kara albashi a Kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel