2019: An shiga takun saka tsakanin jam'iyyar APC da INEC

2019: An shiga takun saka tsakanin jam'iyyar APC da INEC

Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi zargin cewa hukumar zabe mai zaman kanta na kasa (INEC) ta bayyanawa duniya jadawalin zaben fitar da gwani da ta bawa hukumar ba tare da izinin ba kamar yadda Punch ta ruwaito.

Jam'iyyar ta yi wannan zargin ne a wata sanarwa da ta fito daga bakin sakataren yada labaran ta, Mr Yekini Nabena a yau Juma'a a babban birnin tarayya Abuja.

Jam'iyyar ta shawarci INEC ta yi ta dauki matakan gyara don gano jami'anta da ke fitar da irin wannan bayanan ba kan ka'ida ba.

2019: APC tayi kaca-kaca da INEC saboda yi mata tonon silili

2019: APC tayi kaca-kaca da INEC saboda yi mata tonon silili

Kazalika, jam'iyyar ta nuna rashin jin dadin ta kan yadda hukumar ke sakaci irin wadanan bayanan sirri ke fadawa hannun wadanda bai dace ba kuma ta ce ba za ta cigaba da amincewa da irin wannan ba.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2019 a watan Satumba

"Muna kira da babban murya ga INEC ta yi garambawul a sashin jami'an da ke kula da sakonni saboda kiyaye faruwar haka a gaba," inji sanarwan.

Sanarwan ya cigaba da cewa jam'iyyar APC ta aike wa INEC ta jadawalin zaben fitar da gwanin ne don yin biyaya da sashi na 85 na dokar zabe na shekarar 2010.

Jam'iyyar ta shawarci jama'a da suyi watsi da jadawalin zaben da INEC ta fitar domin jam'iyyar na da ikon canja ranakun idan tana bukatar yin hakan.

Anyi kokarin kiran kwamishina yada labarai da wayar da kan masu kada kuri'a na hukumar, Mr Solomon Soyebi da kuma Direktan wayar da kan masu zabe da hulda da jama'a, Mr Oluwole Osaze-Uzzi amma basu amsa wayar ba.

A bangarensa, sakataren yada labarai na INEC, Mr Rotimi Oyekanmi ya shaida wa kamfanin dilllancin labarai NAN cewa ba zai iya tsokaci a kan lamarin ba saboda bashi da cikaken bayani kan abinda ya faru.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel