Wasu jiga-jigan APC za su koma PDP bayan Akpabio ya sauya-sheka zuwa APC

Wasu jiga-jigan APC za su koma PDP bayan Akpabio ya sauya-sheka zuwa APC

Tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom Obong Victor Attah ya bayyana cewa Jam’iyyar APC na iya gamuwa da cikas a zabe mai zuwa na 2019 bayan Sanata Godswill Akpabio ya dawo Jam’iyyar mai mulkin kasar.

Wasu jiga-jigan APC za su koma PDP bayan Akpabio ya sauya-sheka zuwa APC

APC ta shiga rikici a Akwa-Ibom bayan sauyin shekan Akpabio

Obong Victor Attah mai shekaru 79 ya bayyanawa manema labarai cewa idan har Jam’iyyar APC ta sa rai tsohon Gwamna Godswill Akpabio zai kai ta ga ci a 2019, to za ta sha mamaki domin kuwa tsohon Gwamnan ba zai iya komai ba.

Tsohon Gwamnan yace ficewar da Godswill Akpabio yayi daga PDP zuwa APC za ta kawowa Jam’iyyar cikas domin kuwa dole wasu jiga-jigan APC da ake ji da su za su fice su bar Jam’iyyar. Attah yace APC za ta rasa kusoshin ta zuwa PDP.

KU KARANTA: An yi wa Shugaban kasa Buhari alkawarin kuri'u a 2019

Bayan nan dai tsohon Gwamnan Jihar yayi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ceto Miss Leah Shuaibu wanda ta ke hannun ‘Yan Boko Haram. Attah ya kuma yi gargadi game da yunkurin da ake yi na fasa yi wa Najeriya garambuwal.

Kwanan nan Tsohon Gwamnan Jihar Akwa-Ibom watau Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa APC za ta karbe Jihar ta Akwa-Ibom a zabe mai zuwa na 2019. Ba a dade da Sanata Godswill Akpabio ya sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC mai mulki ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel