'Kungiyar wata Jam'iyya na goyon bayan Shugaba Buhari, ta sha alwashin kawo kuri'u 16m a Zaben 2019

'Kungiyar wata Jam'iyya na goyon bayan Shugaba Buhari, ta sha alwashin kawo kuri'u 16m a Zaben 2019

Shugaban wata kungiya ta jam'iyyar Labour Party, Dakta Mike Omotosho, ya sha alwashi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, kan cewar jam'iyyar za ta bayar da gudunmuwar kuri'u miliyan 16 a zaben 2019.

Sai dai kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, shugaban jam'iyyar ya gindaya sharadi ga shugaba Buhari kan cewar wannan alkawari ba zai tabbatu face ya na da tsare da muhimman shirye-shirye na gyaran kasar da za su amfani al'umma baki daya.

Ba bu wani mafificin lamari da jam'iyyar ta sanya a gaba face kyautatawa al'ummar kasar nan da inganta jin dadin su kamar yadda Mista Omotosho ya bayyana.

Omotoshon ya bayyana hakan ne cikin babban birnin Ilorin na jihar Kwara yayin bikin kaddamar da masulhunta na jam'iyyar reshen jihar ta Kwara.

'Kungiyar wata Jam'iyya na goyon bayan Shugaba Buhari, ta sha alwashin kawo kuri'u 16m a Zaben 2019

'Kungiyar wata Jam'iyya na goyon bayan Shugaba Buhari, ta sha alwashin kawo kuri'u 16m a Zaben 2019

Ya kuma bayyana cewa, babu gazawa ko rashin yiwuwa na jam'iyyar ta riki Buhari a matsayin dan takarar ta matukar zai saudaukar da kansa wajen kyautatawa gami inganta jin dadin al'ummar kasar nan.

KARANTA KUMA: Keyamo ya yi kaca-kaca da Obasanjo, Umaru, Jonathan

Wasu jiga-jigan 'yan siyasa da suka halarci wannan biki sun hadar da; 'yan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar APC, Alhaji Yaman Shu'aib da Farfesa Oba Abdulraheem, wani jigo na jam'iyyar APC, Mista Kunle Sulyman, Simeon Ajibola, Iyiola Oyedepo, Bashir Bolarinwa da kuma Saheed Popoola.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel