Makiyaya na shirin kashe ni - Ortom

Makiyaya na shirin kashe ni - Ortom

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, a ranar Juma’a yayi zargin cewa makiyaya sun kammala shirye-shirye domin kai masa harin bazata sannan su kashe shi a babban titin Makurdi/Lafia.

Ortom yayi bayanin cewa ya samu rahoton kwararru game da shirin na yin garkuwa tare da kashe shi.

Makurdi/Lafia it ace hanya guda da zai iya sada mutum da babban birnin tarayya Abuja.

Gwamnan ya bayyana hakan a lokacin wani taron tattaunawa da coci, da hukumar gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki akan yin zaben 2019 cikin lumana wanda kungiyar Makurdi Catholic Diocese ta shirya a Makurdi, babban birnin jihar Benue.

Makiyaya na shirin kashe ni - Ortom

Makiyaya na shirin kashe ni - Ortom

Gwamnan wadda yayi Magana cikin harshen Tiv ya bayyana cewa ya samu rahoton kwararru wanda ya nuna cewa makiyaya wadanda ke mamaye yankunan karamar hukumar Guma dake jihar sun kammala shirin kai masa hari a hanyar Abuja-Lafia.

KU KARANTA KUMA: Abubuwan ban mamaki da yan siyasa keyi kafin zabe (hotuna) Abubuwan ban mamaki da yan siyasa keyi kafin zabe (hotuna)

Ortom ya kuma yi zargin cewa wasu yan asalin Benue sun hada baki da hukumomin tsaro a Abuja domin su kashe shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel