Keyamo ya yi kaca-kaca da Obasanjo, Umaru da Jonathan

Keyamo ya yi kaca-kaca da Obasanjo, Umaru da Jonathan

Mista Festus Keyamo, fitaccen lauyan nan kuma shugaban sadarwa na kungiyar yakin zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa gwamnatocin da suka shude sun yi tabargaza ta hanyar ta'adi ga arzikin ƙasa.

Keyamo ya na tuhumar shugabannin da suka shude wajen yashe dukiya da albarkatun ƙasar nan domin cimma burika na azurta kawunan su ba tare da la'akari da barazanar da hakan zai jefa takalawan ƙasar ba.

Keyamo ya yi kaca-kaca da Yar'Adua, Obasanjo da Jonathan

Keyamo ya yi kaca-kaca da Yar'Adua, Obasanjo da Jonathan

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, Lauyan ya bayyana hakan ne yayin bikin kaddamar masulhunta mazabu da kananan hukumomi a babban birnin Ilorin na jihar Kwara.

KARANTA KUMA: Gwamnatin ka ta ƙara Talauci da rashin aikin yi - Jam'iyyar ADC ga Buhari

Babban Lauyan ya tafi akan cewa, tsawon shekaru 16 na jagorancin gwamnatocin da suka shude ya kafa wani mummunan tsari na wawushe dukiyar da albarkatun kasar nan.

Legit.ng ta fahimci cewa, gwamnatocin da suke shekaru 16 da suka gabata sun hadar da ta; Dakta Goodluck Jonathan; Marigayi Umaru Musa Yar'Adua da kuma Cif Olusegun Obasanjo.

Ya kara da cewa, shugaba Buhari yana iyaka bakin kokarin sa wajen tattalin dukiyar kasar nan inda gudunmuwar da bayar a kasar cikin shekaru uku ta zarce ta shekaru 16 na gwamnatocin da suka gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit

Mailfire view pixel