Kazamar zanga-zangar dalibai ta ja an rufe wata jami'ar Arewa

Kazamar zanga-zangar dalibai ta ja an rufe wata jami'ar Arewa

- An rufe jami'ar noma ta garin Makurdi

- Dalibai ne suka yi zanga-zanga

- Kisan dalibi ne ya ja zanga-zangar

Mahukunta a jami'ar koyon kimiyyar noma dake a garin Makurdi, babban birnin jihar Benue dake a Arewacin Najeriya sun rufe jami'ar har sai baba ta gani sakamakon wata kazamar zanga-zangar data barke.

Kazamar zanga-zangar dalibai ta ja an rufe wata jami'ar Arewa

Kazamar zanga-zangar dalibai ta ja an rufe wata jami'ar Arewa

KU KARANTA: Wasu 'yan kudu sun yi wa Buhari alkawarin kuri'un su

Zanga-zangar daliban dai ta biyo bayan mutuwar daya daga cikin daliban jami'ar mai suna Joseph Odeh sakamakon hadarin motar da ya rutsa da su lokacin da tayar motar da yake ciki ta fashe a kan hanyar su ta zuwa makaranta.

Legit.ng ta samu cewa daliban jami'ar dai sun zargi mahukuntan makarantar ne da kin bashi kyakkyawar kulawa cikin gaggawa da suke tunanin hakan ne yayi sanadiyyar ajalin na sa.

A wani labarin kuma, Yayin da zabukan gama-gari na shekarar 2019 ke cigaba da karatowa, jama'ar kananan hukumomin Ukwa ta gabas da kuma ta Arewa dake a jihar Abia sun yi wa shugaba Buhari alkawarin ruwan kuri'un su a zabukan masu zuwa.

Majiyar mu ta ruwaito mana cewa al'ummar kananan hukumomin dai sun yi wannan alkawarin ne lokacin da tawagar wani masoyin shugaban kasar a jihar mai suna Ikechi Emenike ta kai masu ziyarar rangadi a karshen satin da ya gabata.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel