Zaben 2019: Al'ummar wata jiha a kudu sun yiwa Shugaba Buhari alkawarin kuri'un su

Zaben 2019: Al'ummar wata jiha a kudu sun yiwa Shugaba Buhari alkawarin kuri'un su

- Wasu 'yan kudu sun yiwa buhari alkawarin kuri'un su a 2019

- Sunce Buhari ya cancanci ya zarce

- Sun nuna gamasuwa da salon mulkin sa

Yayin da zabukan gama-gari na shekarar 2019 ke cigaba da karatowa, jama'ar kananan hukumomin Ukwa ta gabas da kuma ta Arewa dake a jihar Abia sun yi wa shugaba Buhari alkawarin ruwan kuri'un su a zabukan masu zuwa.

Zaben 2019: Al'ummar wata jiha a kudu sun yiwa Shugaba Buhari alkawarin kuri'un su

Zaben 2019: Al'ummar wata jiha a kudu sun yiwa Shugaba Buhari alkawarin kuri'un su

KU KARANTA: Jahohi 2 da APC ke hari a shiyyar Jonathan

Majiyar mu ta ruwaito mana cewa al'ummar kananan hukumomin dai sun yi wannan alkawarin ne lokacin da tawagar wani masoyin shugaban kasar a jihar mai suna Ikechi Emenike ta kai masu ziyarar rangadi a karshen satin da ya gabata.

Legit.ng ta samu haka zalika cewa al'ummar kananan hukumomin sun bayyana cewa tabbas shugaba Buhari din ya cancanci ya zarce a zaben mai zuwa idan akayi la'akari da irin cigaban da ya samarwa 'yan Najeriya.

A wani labarin kuma, Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta bayyana cewa akalla manyan ayyuka 69 ne take kan yi a yanzu haka a yankin kudu maso gabashin kasar nan.

Ministan yada labarai, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a lokacin da yake kokarin karyata masu cewa shugaba Buhari bai yi wa yankin na kudu maso gabashin kasar nan komai ba tun bayan hawan sa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel