Yanzu-Yanzu: Mafusatan daliban jami'a sun kona ofishin 'yan sanda bayan kisan dan makarantar su

Yanzu-Yanzu: Mafusatan daliban jami'a sun kona ofishin 'yan sanda bayan kisan dan makarantar su

- Mafusatan dalibai sun kona ofishin yan sanda

- Sun zargi yan sandan da kashe dan uwan su

- Da daren Alhamis ne kisan ya auku

Mafusatan daliban jami'a a garin Iwo, na jihar Osun sun gudanar da zanga-zanga tare da kona ofishin 'yan sandan dake a garin biyo bayan zargin kisan wani dan makarantar su mai suna Tunde Nofiu da suka ce yan sandan rundunar nan na musamman watau Anti Robbery Squad (SARS).

Yanzu-Yanzu: Mafusatan daliban jami'a sun kona ofishin 'yan sanda bayan kisan dan makarantar su

Yanzu-Yanzu: Mafusatan daliban jami'a sun kona ofishin 'yan sanda bayan kisan dan makarantar su

KU KARANTA: Jam'iyyar PDP ta gwalashe Sanata Kwankwaso

Bayanan farko-farko da muka samu game da lamarin sun nuna cewa 'yan sandan sun kashe dalibin ne da yammacin ranar Alhamis din da ta gabata inda su kuma daliban suka shirya kan su suka kuma kona ofishin na 'yan sandan garin.

Legit.ng ta samu cea Kwamishinan yan sandan jihar ta Osun mai suna Mista Finihan Adeoye ya tabbatar da faruwar lamarin amma yace ba zai iya bayar da karin bayani ba game da ainihin abun da ya faru sai ya samu rahoto kan hakan.

A wani labarin mai kama da wannan kuma, Mahukunta a jami'ar koyon kimiyyar noma dake a garin Makurdi, babban birnin jihar Benue dake a Arewacin Najeriya sun rufe jami'ar har sai baba ta gani sakamakon wata kazamar zanga-zangar data barke.

Zanga-zangar daliban dai ta biyo bayan mutuwar daya daga cikin daliban jami'ar mai suna Joseph Odeh sakamakon hadarin motar da ya rutsa da su lokacin da tayar motar da yake ciki ta fashe a kan hanyar su ta zuwa makaranta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel