Jahohi 2 da jam'iyyar APC ke shirin kwata a shiyyar tsohon shugaba Jonathan

Jahohi 2 da jam'iyyar APC ke shirin kwata a shiyyar tsohon shugaba Jonathan

- APC na harin jahohi 3 a kudu lokacin zabe mai zuwa

- APC tace ta shirya tsaf domin ansar jahohin daga PDP

- Tsohon gwamnan Delta da Akwa Ibom sun koma APC

Jam'iyyar mai mulki a tarayyar Najeriya ta All Progressives Congress (APC) ta bayyana aniyar ta ta kara mamaye yankunan jahohin Najeriya inda suka kuduri aniyar cafkar jahohi akalla uku daga bangaren kudu maso kudancin Najeriya a zaben gama gari na 2019.

Jahohi 2 da jam'iyyar APC ke shirin kwata a shiyyar tsohon shugaba Jonathan

Jahohi 2 da jam'iyyar APC ke shirin kwata a shiyyar tsohon shugaba Jonathan

KU KARANTA: Batun shiga Kano: Kwankwaso ya maidawa Ganduje martani

A halin yanzu dai, jam'iyyar ta APC a kudu maso kudancin kasar ta tana mulki ne a jiha daya tilo ta Edo dake zaman jihar da shugaban ta na yanzu watau Adams Oshiomhole ya fita daga cikin ta.

Legit.ng ta samu cewa jam'iyyar ta All Progressives Congress, APC yanzu haka tana ta shirin ganin ta karbi jahohin Akwa Ibom da Delta ne a zaben mai zuwa shi yasa ma suka yi zawarcin tsohon gwamnan jihohin Akwa Ibom da Delta, Godswill Akpabio da Emmanuel Uduaghan.

A wani labarin kuma, Shugaban gwamnonin jahohin Najeriya a karkashin inuwar jam'iyyar APC kuma gwamnan jihar Imo dake a shiyyar kudu maso kudancin kasar nan, Rochas Okorocha ya yi ikirarin cewa a cikin gwamnatin shugaba Buhari, akwai ikon Allah da dama.

Gwamna Rochas yayi wannan ikirarin ne lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya jagoranci sauran gwamnonin jam'iyyar a wata tattaunawar sirri da sukayi da shugaba Buhari a garin Daura.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel