Gwamnatin ka ta ƙara Talauci da rashin aikin yi - Jam'iyyar ADC ga Buhari

Gwamnatin ka ta ƙara Talauci da rashin aikin yi - Jam'iyyar ADC ga Buhari

Jam'iyyar ADC (African Democratic Congress), ta hau kujerar naƙi ta rashin amincewa da da'awar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bayyana cewa, 'yan adawar sa ba su da ta cewa kan gazawa ko naƙasun gwamnatin sa.

Shugaban kasar ya bayyana cewa, 'yan adawa ba su da ta cewa kan gazawar gwamnatin sa musamman ta fuskar tsaro, tattalin arziki da kuma yakin da cin hanci a rashawa.

Cikin wata sanarwa da hannun kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a mahaifarsa ta garin Daura dake jihar Katsina a ranar Alhamis din da ta gabata.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, shugaba Buhari ya bayyana cewa zai ci gaba da jajircewa kamar yadda aka sani wajen sauke nauyin jagorancin kasar nan da Mai Duka ya rataya a wuyansa.

Gwamnatinka ta ƙara Talauci da rashin aikin yi - Jam'iyyar ADC ga Buhari

Gwamnatinka ta ƙara Talauci da rashin aikin yi - Jam'iyyar ADC ga Buhari

A yayin bayyana rashin amincewar sa da ikiraran shugaban kasa, Shugaban jam'iyyar, Cif Okey Nwosu ya bayyana cewa, akwai ban takaici dangane da yadda shugaba Buhari ya maishe da kujerar sa ta shugaban kasa tamkar wata masana'anta ta buga karairayi da shaci fadi.

KARANTA KUMA: 'Yan Fashi da Makami sanye cikin Kayan Dakarun Soji sun tsere daga hannun 'Yan Sanda

Nwosu, wanda jam'iyyar sa ta samu sahalewar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, ƙididdiga gami da bincike na gaskiya da sanadin cibiyoyin gwamnati ya tabbatar da cewa talauci gami da rashin aikin yi sun ƙara kaiwa wani munzalin a gwamnatin shugaba Buhari.

Shugaban jam'iyyar ya ƙara da cewa, rikici gami da tashin-tashin ya kai intaha a musamman a yankunan Najeriya ta Tsakiya a wannan gwamnati da shugaba Buhari ke ci gaba da yaudarar al'ummar kasar nan da da'awar ya shawo kan matsalar tsaro.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel