Tsohon dan majalisa tare da mambobin APC 300 sun sauya sheka zuwa PDP a Ebonyi

Tsohon dan majalisa tare da mambobin APC 300 sun sauya sheka zuwa PDP a Ebonyi

Akalla mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) karkashin jagorancin wani tsohon dan majalisar dokokin kasar, Bede Nwali, ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic party (PDP) a jihar Ebonyi a jiya.

Da yake Magana a madadin sauran masu sauya sheka a sakatariyar jam’iyyar na jihar, Abakaliki, Nwali wanda yayi godiya ga shugabanni da mambobin jam’iyyar PDP a karamar hukumar Ebonyi na jihar kan yadda suka karbe su hannu biyu-biyu, ya basu tabbacin samun goyon bayansu da jajircewa a zaben 2019.

Yace sun yanke shawarar komawa jam’iyyar PDP ne saboda nasarori da cigaba da gwamnatinta ta kawo ga mutane a Ebonyi cikin kasa da shekaru uku da hawa mulki.

Tsohon dan majalisa tare da mambobin APC 300 sun sauya sheka zuwa PDP a Ebonyi

Tsohon dan majalisa tare da mambobin APC 300 sun sauya sheka zuwa PDP a Ebonyi

Da yake tarban masu sauya shekar, shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Barista Onyekachi Nwebonyi yayi masu godiya kan matakin da suka dauka na komawa jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar matasan Arewa ta gargadi Miyetti Allah akan barazanar tsige Saraki daga kujerarsa

Ya bukaci masu sauya shekar da su kwantar da hankalinsu sannan su yi tarayya da sauran mambobin jam’iyyar kamar yadda ya bayyana cewa jam’iyyar na kula da soyayya da hadin kan damokradiyya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel