'Yan Fashi da Makami sanye cikin Kayan Dakarun Soji sun tsere daga hannun 'Yan Sanda

'Yan Fashi da Makami sanye cikin Kayan Dakarun Soji sun tsere daga hannun 'Yan Sanda

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito mun samu rahoton cewa, wasu 'yan ta'adda da ake zargin 'yan fashi da makami ne sun tsere daga hannun hukumar 'yan sanda sanye cikin kaya irin na Dakarun Soji a jihar Anambra.

Aukuwar wannan lamari a ranar Alhamis din da ta gabata ya sanadiyar dimuwa gami da tashin hankali a gari Obosi dake karamar Hukumar Idemili ta Arewa a jihar, inda 'yan ta'addan uku suka kuɓuce daga ɗakin kurkuku na ofishin 'yan sanda.

Wannan 'yan ta'adda, Olisa Dominic, Friday Nwali da kuma Nwanosike Isaac, sun shiga hannun 'yan kungiyar sa kai yayin da suke shirin kai farmaki a yankin Obosi Vanguard dake unguwar Little Wood Estate.

Rahotanni da sanadin kafar watsa labarai ta Southern City News ta bayyana cewa, wannan 'yan ta'adda sun kuɓuce bayan da ƙungiyar sa kai da danƙa su a hannun jami'an tsaro na 'yan sanda.

Wata majiya da ta buƙaci a sakaya sunanta ta shaidawa manema labarai cewa, a halin yanzu al'ummar yankin Obosi na ci gaba da zaman ɗar-ɗar sakamakon aukuwar wannan mummunan lamari mai cike da takaici da ban mamaki.

Majiyar ta ci gaba da cewa, ko baccin kirki ba su samu sakamakon fargaba abin da ka iya biyo bayan wannan lamari mai cike da rashin yarda.

KARANTA KUMA: 'Kasar Afirka ta Kudu ta datse wani Babban Tarago daga 'Kasar Rasha ɗauke da muggan Makamai zuwa Najeriya

A yayin ganawar sa da manema labarai, shugaban kungiyar sa kai, Mista Oluchukwu Anyaoku, ya bayyana cewa ya samu rahoton wannan lamari inda ya tura mataimakin sa, Chimezie Ononwu, wanda ya danƙa 'yan ta'addan a hannun jami'an domin gudanar da bincike a ofishin su na Ogidi.

Yayin bayyana takaicin sa, kwamishinan 'yan sanda na jihar, Mista Garba Umar, ya bayar da umarni ga jami'an sa domin tsananta binciken diddigi akan wannan lamari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel