Rikicin siyasa ya jawo an sa takun-kumi a Jihar Bayelsa

Rikicin siyasa ya jawo an sa takun-kumi a Jihar Bayelsa

Shugaban Karamar Hukumar Brass da ke Jihar Bayelsa Victor Issaih ya sa dokar ta-baci bayan rikicin siyasa ya barke inda har ta kai ga rashin wasu mutane 3 babu gaira babu dalili farkon makon nan.

Rikicin siyasa ya jawo an sa takun-kumi a Jihar Bayelsa

An kashe mutane a Bayelsa wajen rikicin PDP da APC

Victor Issaih ya sa takun-kumin fita tsakanin karfe 9:00 na dare har zuwa 6:00 na safiya saboda rikicin da ya barke tsakanin magoya bayan Jam’iyyar APC da kuma na Jam’iyyar PDP. Rigimar ta ja an rasa mutane har 3 a Ranar Litinin dinnan.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Daily Trust, Shugaban Karamar Hukumar yayi tir da wannan aika-aika inda yace babu hannun Jam’iyyar sa ta PDP wajen wannan rikici. Issaih yace shi ma an yi kokarin ganin bayan sa sa’ilin da ake rikicin.

KU KARANATA: Ma'aikatan Ekiti sun shiga wani danyen yajin aiki

Victor Issaih yace an kawo masa hari da manyan makamai inda yace Ubangiji ne ya cece sa. Issaih ya zargi manyan APC a Jihar da hannu cikin wannan barna. Issaih yace wani ‘Dan Majalisan Jihar Sunny Goli ne ya kitsa wannan mugun aiki.

Har wa yau, Shugaban Karamar Hukumar ya bayyana cewa ‘Yan APC na amfani da wani fitinanen Tsagera da aka sani da Kelvin Ikurusi wajen tada rikici a Jihar. Ikurusi wani rikakken ‘Dan daba ne da yanzu ya gagari Jami’an tsaro a Bayelsa.

APC dai ta zare hannun ta a wannan rikici inda ta aikawa Sufeta Janar na ‘Yan Sanda takarda cewa an kashe mutanen ta a Jihar ta Bayelsa. ‘Dan Majalisar APC da ake zargi da wannan abu shi ma yace sharrin PDP ne na hana ‘Yan adawa sakat.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel