An gano Mahajjatan Najeriyan da su ka nemi su bace bayan aikin Hajji

An gano Mahajjatan Najeriyan da su ka nemi su bace bayan aikin Hajji

Mun samu labari cewa an gano Alhazan Najeriyan da su ka nemi su bace yayin da aka kammala aikin Hajji na bana. A jiya Jaridar Yerwa Express ta rahoto cewa wasu Mahajjatan Borno sun bace.

An gano Mahajjatan Najeriyan da su ka nemi su bace bayan aikin Hajji

Wasu Alhazan Borno sun nemi su bace a Garin Makkah

Sai dai kamar yadda mu ka samu labari, jim kadan bayan an fitar da wannan rahoto ne aka tabbatar da cewa an gano wadannan Alhazai na Jihar Borno da su ka bace a kan hanyar su zuwa babban Birnin Makkah daga Garin Minna.

Yerwa Express ta bayyana cewa fiye da sa’a 6 bayan Mahajjata sun dawo gidajen su a Makkah, an nemi wasu Alhazai 52 da su ka fito daga shiyar Jihar Borno an rasa, ko da cewa dai tafiya daga Minna zuwa Makkah babu wani nisa.

KU KATANAYA: Wani 'Dan Najeriya yayi abin kirki a Kasa mai tsarki

Wanda ya ke da masaniya game da abin da ya faru ya bayyana cewa wanda yake tafe da Mahajjatan ne bai san hanya ba, hakan ya jawo Alhazan na Najeriya su kayi ta gararamba a tafiyar da ba ta wuce rabin sa’a a lafiyyyar mota ba.

Jami’an Alhazai dai sun tabbatar da cewa yanzu Mahajjatan duk sun dawo otel din su a Garin Makkah kamar yadda ya kamata. Rahoton da Jaridar ta fitar ne ya zaburar da Jami’an aikin Hajji na kasar wajen ganin an gano Mahajjatan.

Kun san cewa Mahajjatan bana dai sun biya sama da Naira Miliyan daya da rabi. Majalisar Tarayya ta koka da tsadar kujerun jirgin don haka ta nemi Gwamnati tayi rangwame amma bai yiwu ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel