Kotu ta ci tarar Janar Tukur Buratai Naira Miliyan 11

Kotu ta ci tarar Janar Tukur Buratai Naira Miliyan 11

- Kotu ta ci tarar Janar Tukur Buratai tarar Naira Miliyan 11

- Mai shari'a Ijeoma ta ce za'a raba kudin ga matasa 11 da rundunar soji taci zarafinsu a Gombe

- Rundunar soji ta tsare matasan ne tun daga 6 ga watan Yuni

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta ci tarar hafsan hafsoshin sojin Nigeria zunzurutun kudi Naira Miliyan 11, biyo bayan hukuncin da kotun ta yanke, akan shari'ar cin zarafin da rundunar soji sukayiwa al'umar garin Shongom dake jihar Gombe.

Wanan hukunci da mai shari'a Justice Ijeoma Ojukwu ta yanke akan Janar Tukur Buratai, zai baiwa matasa 11 da rundunar soji taciwa zarafin damar raba Naira Miliyan 11 a tsakaninsu.

Da ta ke yanke hukunci, mai shari'a Justice Ijeoma Ojukwu, ta ce: "Irin yadda dakarun sojin Janar Tukur Buratai suka ci zarafin matasan 11 a gombe, ta hanyar tsare su tun daga makon farko na watan Yuni, tare da yi musu azaba, ya fita daga tsarin mulki na kasar".

Kotu ta ci tarar Janar Tukur Buratai Naira Miliyan 11

Kotu ta ci tarar Janar Tukur Buratai Naira Miliyan 11

KARANTA WANNAN: Hajjin bana: An kama wani dan arewacin Najeriya a Saudiyya saboda dukan dan sanda

Daga karshe mai shari'ar ta baiwa rundunar sojin umarnin gaggawa na sallamar matasan 11, tare da basu diyyar Naira Miliyan daya kowanne, sakamakon cin zarafinsu da akayi.

Lamarin ya samo asali ne tun a lokacin da matasan suka tsinci gawar daya daga cikin su a cikin gonarsu, a kan hanyar ta maida gawar gida ne rundunar soji ta yi awon gaba da su tun daga ranar 6 ga watan Yuni.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel