Sauya shekar Gwanonin APC yayi mana ciwo sosai - Okorocha

Sauya shekar Gwanonin APC yayi mana ciwo sosai - Okorocha

- Gwamnan jihar Imo ya nuna cewa sun ji takaicin barin jam'iyyar APC da wasu gwamnoni suka yi

- Ya bayyana ra'ayinsa a taron ciun abinci da suka yi tare da shugaba Buhari a Daura

- Okorocha yace hakan ba yana nufin sauya shekarsu zai shafi jam'iyyar bane

Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo, a ranar Alhamis, 23 ga watan Agusta ya bayyana cewa sauya shekar wasu gwamnoni kuma mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) yayi masu ciwo sosai.

Ya bayyana hakan a Daura, jihar Katsina lokacin da ya jagoranci sauran gwamnonin APC wajen ziyarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin bikin babban Sallah tare da shi.

“Muna fatan dama ace babu wanda ya bar jam’iyyar daga cikinsu musamman gwamnoni. Muna da buri kuma hakan yayi mana ciwo sosai,” inji Okorocha wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar.

Sauya shekar Gwanonin APC yayi mana ciwo sosai - Okorocha

Sauya shekar Gwanonin APC yayi mana ciwo sosai - Okorocha

Yayi bayanin cewa ciwon da abun yayi masu ya kasance saboda sunyi tarayya da juna a matsayin yan uwa.

KU KARANTA KUMA: Jama'a su yi hattara da yan a mutu ko ayi ran siyasa - Nnamani

Kawai sai a wayi gari ka ga babu wani naka, mun ji lamarin, inji shi.

Gwamnan na martani ne ga sauya shekar wasu mambobin jam’iyyar musamman na Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue; Abdulfatah Ahmed na jihar Kwara; da kuma Aminu Tambuwal na jihar Sokoto.

Dukkanin gwamnonin uku sun sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party cikin mako guda, farko Ortom a ranar 25 ga watan Yuli, Ahmed a ranar 31 ga watan Yuli sannan kuma Tambuwal a ranar 1 ga watan Agusta.

Duk da cewar da yayi abun yayi masu ciwo, Okorocha yace hakan ba zai shafi nasarar jam’iyyarsu ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel