Yanzu Yanzu: Wani dan Nigeria ya kashe dan kasarsa a Afrika ta Kudu

Yanzu Yanzu: Wani dan Nigeria ya kashe dan kasarsa a Afrika ta Kudu

- Wani dan Nigeria ya gamu da ajalinsa biyo bayan sa-in-sa da wani dan Nigeria a Afrika ta Kudu

- Kungiyar NUSA ta roki hukumomin tsaro dana fannin shari'a da su gurfanar da mai laifin a gaban shari'a

- Wannan ne karo na biyu da yan Nigeria ke kashe yan uwansu a kasar Afrika ta Kudu

Al'umar Nigeria mazauna kasar Afrika ta Kudu, sun yi Allah wadai da kisan wani dan Nigeria mai shekaru 28, Okolie Olileanyi Paul, dan asalin karamar hukumar Awgu Local Government, a jihar Enugu, wanda ya gamu da ajalinsa a hannun wani dan Nigeria mazaunin kasar.

Sakataren watsa labarai na kasa, a kungiyar yan Nigeria mazauna Afrika ta Kudu, NUSA, Chief Iyke Odefe, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar alhamis, ya ce marigayin ya gamu da ajalinsa ne bayan da wani dan Nigeria kuma makwafcinsa, Mr. Donald Mordi, dan asalin karamar hukumar Ika ta arewa maso gabas, jihar Delta, ya caka masa wuka.

Mr. Odefe ya ce: "Ya caka masa wuka ne yayin da suke yin wata sa-in-sa, wacce har ta kaisu ga fara kokowa. Mummunan lamarin ya afku ne a yankin 'Roodenport West Rand', a ranar 17 ga watan Augusta.

KARANTA WANNAN: Hajjin bana: An kama wani dan arewacin Najeriya a Saudiyya saboda dukan dan sanda

"Wanda yayi kisan ya tsere tun a wannan rana, jami'an tsaro na 'yan sanda na kan farautarsa. Haka zalika muma a kungiyance muna kan taka muhimmiyar rawa. Muna rokon jami'an tsaro da fannin shari'a, da su tabbatar sun gurfanar da wanda yayi wannan aika aikar don fuskantar shari'a.

Daga karshe muna mika sakon ta'aziyarmu ga iyalai, 'yan uwa da abokan mamacin."

Idan za'a iya tunawa, Legit.ng ta kawo maku rahoto kan kisan da akayiwa wani dan Nigeria mai shekaru 42, Mr. Chibuzor Nwankwo, wanda wani dan Nigeria, Lawrence Nwarienne, ya harbeshi da bindiga a ranar 27 ga watan Yuli, a Kempton Park, Johannesburg.

Rahoton ya bayyana cewa Mr. Nwarienne ya kashe mamacin ta hanyar harbinsa da bindiga ba tare da an san dalilin yin hakan ba. To sai dai tuni 'yan sanda suka cafke shi, tare da gudanar da bincike akan kisan kan da yayi

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel