Jama'a su yi hattara da yan a mutu ko ayi ran siyasa - Nnamani

Jama'a su yi hattara da yan a mutu ko ayi ran siyasa - Nnamani

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani ya gargadi yan Najeriya da su hankalta da yan siyasar ko a mutu wadanda basu da adireshi na biyu.

Nnamani ya bayar da gargadi ne a yayin wata hira da manema labarai na fadar shugaban kasa, bayan ganawa da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Vanguard ta ruywaito.

Legit.ng ta tattaro cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, wadda ya kasance jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya kuma shawarci yan siyasa masu fafutuka da su mallaki adireshi na biyu.

Nnamani ya samu rakiyan, Cif Emeka Offor, wanda ya ce ya kawo masu hannun jari daga kasar Turai domin su gana da Osinbajo akan damar zuba jari a mai, gas, da hukumomin wutar lantarki.

Jama'a su yi hattara da yan a mutu ko ayi ran siyasa - Nnamani

Jama'a su yi hattara da yan a mutu ko ayi ran siyasa - Nnamani

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Sanata Shehu Sani (APC-Kaduna ta tsakiya) ya bayyana cewa ba wai don an magance rikicinsa da shugabancin jam’iyyar na jihar Kaduna ba ne yasa shi ci gaba da kasancewa a jam’iyyar ba, sai dai saboda sanya bakin da Shugaba Buhari da shugaban jam’iyyar na kasa suka yi.

KU KARANTA KUMA: Babu wani shugaban kasa a tarihin Najeriya da yayi ma talaka aiki kamar Buhari

Sani ya bayyana hakan a lokacin ziyarar bikin Sallah da ya kaiwa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura, jihar Katsina a ranar Alhamis, 23 ga watan Agusta, NAN ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel