Za a dade ba a manta da Goodluck Jonathan a Najeriya ba - Inji Kwankwaso

Za a dade ba a manta da Goodluck Jonathan a Najeriya ba - Inji Kwankwaso

Mun samu labari cewa Sanatan Kano ta tsakiya Rabiu Musa Kwankwaso ya yabawa tsohon Shugaban Najeriya Dr. Goodluck Jonathan bayan manyan ‘Yan siyasar sun yi wani zama shekaran jiya da dare.

Za a dade ba a manta da Goodluck Jonathan a Najeriya ba - Inji Kwankwaso

Kwankwaso ya jinjinawa tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan

Tsohon Gwamnan na Jihar Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya fito shafin sa na Tuwita jiya ya bayyana cewa idan dai ana maganar shugabannin da su kayi wa Kasar nan hidima, to dole a kira Dr. Goodluck Ebele Jonathan.

Sanata Rabiu Kwankwaso yace ba za a manta da Jonathan a kasar nan ba saboda kokarin da yayi wajen cigaban Najeriya. Kwankwaso yace wannan ne ya sa ya samu lokaci ya zauna da tsohon Shugaban domin ganin cigaban Najeriya.

KU KARANTA: Shehu Sani ya gana da Shugaban kasa Buhari a Daura

Injiniya Rabiu Kwankwaso wanda kwanan nan ya bar jam’iyyar APC ya koma PDP yana kokarin tsayawa takarar Shugaban kasa a zaben 2019 a karkashin Jam’iyyar PDP. Hakan ta sa kwankwaso yake neman goyon bayan manyan PDP.

A 2014 dai an samu sabani tsakanin Kwankwaso lokacin yana Gwamna yayin da Jonathan yake rike da kasar nan. Kwankwaso da wasu Gwamnonin PDP sun fice zuwa Jam’iyyar APC bayan sun yi kaca-kaca da Gwamnatin Jonathan.

Bayan Kwankwaso yayi zama da Jonathan a gidan sa a Maitama, Sanatan ya kuma zanta da tsohon Shugaban kasa Janar Yakubu Gowon a gidan sa da ke Unguwar Asokoro duk a cikin Garin Abuja.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel