2019: Zamu samawa Buhari kuri'u Miliyan 16 -Labour Party

2019: Zamu samawa Buhari kuri'u Miliyan 16 -Labour Party

- Shugaban jam'iyar LP na kasa yasha alwashin tabbatar da kudurin shugaban kasa Buhari na tazarce

- Ya ce jam'iyar zata taya Buhari yakin zabe, da kuma sama mashi kuri'u Miliyan 16

- An bayyana shugaba Buhari a matsayin wanda ya cancanci a sake bashi damar yin tazarce

Jam'iyar Labour Party (LP) ta sha alwashin samawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kuri'u Miliyan 16 a zaben shugabancin kasar na 2019 dake gabatowa.

Shugaban jam'iyar na kasa Dr. Mike Omotosho, shi ne ya bayyana hakan a ranar alhamis a Ilorin, wajen wani taron karawa juna sani tare da kaddamar da jami'an sa kai da zasuyi yakin neman tazarcen shugaba Buhari da mataimakinsa, Prof. Yemi Osinbajo.

2019: Zamu samawa Buhari kuri'u Miliyan 16 -Labour Party

2019: Zamu samawa Buhari kuri'u Miliyan 16 -Labour Party

Taron wanda kungiyar 'Buhari/Osinbajo 2019 Project' ta shirya, ya samu halarcin Alhaji Lai Mohammed, ministan labarai da al'adu, da kuma shugaban jam'iyar APC na jihar Kwara.

KARANTA WANNAN: Hajjin bana: Dan Najeriya ya mayar da fiye da miliyan da ya tsinta a Makkah

A jawabinsa na godiya, Omotosho ya ce, jam'iyar Labour Party zata taya Buhari yakin neman Tazarce, tare da sama mashi kuri'u yayin zaben.

Da ya ke jawabi a wajen taron, shugaban riko na jam'ar APC a jihar Kwara, Bashir Bolarinwa, ya ce: "Shugaban kasa Buhari ya cancanci a bashi damar sake zarcewa shugabancin kasar, don samun damar kammala ayyukan raya kasa da ya sanya a gaba."

Otunba Gani Zubai, kodinetan kungiyar 'Buhari/Osinbajo 2019 Project', ya ce an kafa kungiyar ne biyo bayan rikicin da ya barke a cikin jam'iyar APC, da kuma yawaitar sauya shekar wasu yan majalisun dokoki na kasar daga jam'iyar zuwa wasu jam'iyu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel