Shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2019 a watan Satumba

Shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2019 a watan Satumba

- A karo na farko gwamnatin tarayya za ta gabatarwa majalisa kasafin kudi a watan Satumba

- A tsarin dokar kasa, ya kamata a fara aiki da kasafin kudin ne daga watan Janairu zuwa Disamba

- Sai dai a shekarun da suka gabata, rashin gabatarwa majalisa kasafin kudin kan lokaci ke hana amincewa dashi a kan lokaci

Gwamnatin tarayya za ta gabatar wa majalisar tarayya kasafin kudin shekarar 2019 a watan Satumban shekarar 2018 saboda a samu damar fara aiki da kasafin kudin daga watan Janairu zuwa Disamba kamar yadda ya ke tun farko.

Karamar Ministan Kasafin kudi da tsare-tsare, Hajiya Zainab Ahmed ne ta tabbatar da wannan canjin a wata hira na musamman da tayi da wakilan Daily Trust a babban birnin tarayya Abuja.

Shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudin badi a watan Satumban bana

Shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudin badi a watan Satumban bana

Ministan ta ce gwamnatin tarayya ta tuntubi 'yan majalisar tarayya da dama domin ganin an samu nasarar kawo wannnan muhimmin gyarar.

DUBA WANNAN: Sabuwar rikici ta barke a jam'iyyar PDP a wata jihar Arewa

A shekaru biyu da suka shude, fadar shugaban kasar ba ta iya gabatar da kasafin kudin a watan Janairun ba. Shugaban kasa ya gabatar da kasafin kudin 2017 a majalisa a mako na biyu na watan Disambar 2016 yayin da kasafin na 2018 an gabatar dashi ne a watan Nuwambar 2017.

A yayin da ta ke tsokaci kan wannan yunkurin na gwamnati, Ministan ta ce: "Kokarinmu shine ganin cewa munyi biyaya ga doka ta hanyar gabatarwa majalisa kasafin kudi a watan Satumba tunda majalisar sun tafi hutu amma za su dawo a watan Satumba."

Ta ce dokar kasa yana kwadaitar da fadar shugaban kasa ta gabatarwa majalisar tarayya kasafin kudin a watan Satumba saboda ana sa ran a watan Disamba za'a amince da kasafin kudin.

Ministan kuma ta kara da cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kashe N1.56 tiriliyan a kan manyan ayyuka wanda adadin shine mafi tsoka da gwamnatin tarayya ta taba warewa a tarihin Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel