Kungiyar kwadago ta fatattaki ma’aikata daga ofisoshinsu don a fara yajin aiki sai baba ta ji

Kungiyar kwadago ta fatattaki ma’aikata daga ofisoshinsu don a fara yajin aiki sai baba ta ji

Kungiyoyin kwadago, NLC da TUC sun bi ma’aikata har wuraren ayyukansu a jihar Ekiti, inda suka fatattakesu a kokarin ganin duk wani ma’aikaci a jihar ya shiga yajin aiki har sai illa masha Allahu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kungiyoyin sun kaddamar da wannan yakin aiki na dindindin ne sakamakon rashin biyan albashin ma’aikata na watanni shida zuwa watanni goma da gwamnatin jihar ta yi biris, taki biya.

KU KARANTA: Kalli yadda mayakan Boko Haram suka gudanar da bikin Sallah a dokar daji

Kungiyar kwadago ta fatattaki ma’aikata daga ofisoshinsu don a fara yajin aiki sai baba ta ji

Kungiyar kwadago

Shuwagabannin tafiyar, Kwamared Ayodeji Aluko da kwamared Kolawole Olaiya sun bayyana cewa ba adalci bane ace Gwamna Fayose daya zargi tsohon gwamna Fayemi da nuna halin ko in kula da ma’akata kan bai biya albashin wata daya ba a 2014, ace shine yau ma’aikata ke binshi bashin albashin wata goma.

Sai dayake jagororin shiga wannan yajin aikin tsofaffin shuwagabannin NLC d a TUC ne, don haka ana takun saka ta bulla tsakaninsu da shuwagabannin kungiyoyin masu ci, da suka hada da Ade Adesanmi da Odunayo Adesoye.

An jiyo shuwagabannin suna cewa jagororin tafiya yajin aikin basu da wata manufa ta alheri, suna yi ne kawai don su samu shiga a wajen zababben gwamnan jihar mai jiran gado, Kayode Fayemi, sai dai suma tsofaffain shuwagabannin sun zargi shuwagabannin dake ci da cewa sun karbi naira miliyan 14 daga Fayose don harhada masa kan ma’aikatan gwamnati a yayin zaben gwamnan daya gabata.

Zuwa yanzu dai ana can ana cecekuce, nuna ma juna yatsa tare da murza gashin baki a tsakanin bangarorin biyu, musamman game da inganci da sahihancin wannan yajin aiki da suka daka.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel