2019: PDP ta samu karuwa ta wani dan majalisa da ya fita daga APC

2019: PDP ta samu karuwa ta wani dan majalisa da ya fita daga APC

Dan majalisar dokokin jihar Osun, Mista Clement Akanni, mai wakiltar mazabar Ila ya fita daga jam’iyyar APC mai mulki tare da tsallakawa zuwa jam’iyyar PDP ta adawa.

Da yake bayyana fitar sa daga APC a fadar sarkin garin Ila, Orangun na kasar Ila, Akanni y ace wasu ‘yan adawar sa ne suka kore shi daga jam’iyyar tare da yin korafin cewar an mayar da mazabar sa koma baya a aiyukan da gwamnatin jihar ke yi.

Kazalika ya bayyana cewar duk kokarinsa na kawo kudiri da zai zama alheri ga mutanensa sai wasu daga cikin abokan aikinsa ‘yan APC su dakile yunkurinsa.

2019: PDP ta samu karuwa ta wani dan majalisa da ya fita daga APC

Gwamna Rauf Aregbesola

Akanni ya ciaba da cewa babu amfanin ya cigaba da zama a cikin APC din tunda ba zai iya yin amfani da jam’iyyar domin kawo cigaba ga jama’ar da yake wakilta ba.

A wani rahoton mai nasaba da wannan, Mista Peter Babalola, shugaban hukumar kula da kananan hukumomi kuma jigo a jamiyyar APC a jihar ta Osun ya mika takardar sa ta barin aiki ga gwamna Rauf Aregbesola.

DUBA WANNAN: 2019: Oshiomhole na farautar tsohon gwamnan PDP wurjan-jan zuwa APC

Da yake bayyana dalilinsa na yin murabus a takardar da ya mika ga gwamnan, Babalola, daya daga cikin ‘yan takarar gwamna a APC da Alhaji Gboyega Oyetola ya kayar a zaben cikin gida, y ace ya bar aiki ne domin mayar da hankali a wasu al’amura da ya sa a gabansa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel