Yawan canja jam'iyya na da alaka da matsalar kwakwalwa - Tsohon gwamna Sylva

Yawan canja jam'iyya na da alaka da matsalar kwakwalwa - Tsohon gwamna Sylva

Tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Cif Timipre Sylva ya ce a tunaninsa akwai alaka mai karfi tsakanin son canje-canjen jam'iyya da yawa da matsalar kwakwalwa, ya fadi hakan ne yayin mayar da martani ga jita-jitar cewa ya fice daga APC ya koma PDP.

Tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Timipre Sylva ya ce akwai bukatar a rika duba kwakwale 'yan siyasan da suke canja jam'iyyunsu.

Sylva ya yi wannan furucin ne a ranar Alhamis yayin da yake mayar da martani game da jita-jitan da ake yadawa na cewa ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP.

A duba kwakwalen wadanda suka fiye canja jam'iyyunsu - Sylva

A duba kwakwalen wadanda suka fiye canja jam'iyyunsu - Sylva

A sanarwan da ya fitar ta bakin mai magana da yawunsa, Julius Bokoru, tsohon gwamnan ya yi zargin cewa gwamnatin PDP dake mulki a jiharsa ne ta ke yada jita-jitan.

DUBA WANNAN: Sabuwar rikici ta barke a jam'iyyar PDP a wata jihar Arewa

Slyva ya lashe zabe a karkashin inuwar jam'iyyar PDP ne amma daga baya ya sauya sheka zuwa APC inda ya fadi zabe a shekarar 2016.

Tsohon gwamnan ya sake jadadawa magoya bayansa cewa yana nan daram a jam'iyyar APC kuma ya shawarci wadanda ke yada jita-jitar su farka daga barcin da su keyi.

"Cif Timipre Sylva ya ce akwai alaka mai karfi tsakanin canja jam'iyya barkatai da matsalar kwakwalwa hakan yasa ya ke ganin duk wadanda suka fiye sauya sheka daga wannan jam'iyya zuwa wata suna bukatar a duba lafiyar kwakwalwarsu.

"A yayin da wannan jita-jitar alama ce da ke nuna 'yan jam'iyyar PDP na kwadayin samun dan siyasa mai nagarta a tare dasu, Cif Timipre Slyva yana fata jadada kasancewarsa a APC zai sanya su farka daga barcin da su keyi."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel