Rikicin siyasa ya lakume ran wani dan kungiyar asiri, da yawa sun jikkata

Rikicin siyasa ya lakume ran wani dan kungiyar asiri, da yawa sun jikkata

- Kowa yaki sharar masallaci tabbas yayi ta kasuwa

- A sanadin rigimar siyasa wani matashi ya sheka lahira wasu kuma sun fada halin jiyyar dole

Rikicin siyasa ya yi sanadiyar rasa ran wani matashi tare da jikkata wasu da yawa, a wani rikici da ya faru tsakanin kungiyar asiri ta Eiye da Baggar a unguwar Owa-Oyibu da ke yankin Agbor na jihar Delta.

Rikicin siyasa ya lakume ran wani dan kungiyar asiri tare da jikkata wasu da dama

Rikicin siyasa ya lakume ran wani dan kungiyar asiri tare da jikkata wasu da dama

Rikicin dai ya samo asali ne bayan da wani jigon siyasa da ba'a ambaci sunansa ba ya sauya sheka daga jam’iyyar da yake ciki zuwa wata.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa an fara rikicin ne sakamakon wata gardama da ta barke tsakanin ‘yan kungiyar asirin a lokacin da suke tsaka da caca.

Jim kadan da barkewar rikicin ne, ‘yan kungiyar asirin su ka fara fito da muggan makamai tare da fara karon batta, hakan ya zamo sanadiyyar mutuwar mutum guda tare da jikkata wasu da dama.

KU KARANTA: Wani maigida ya hada baki da Likita wajen cirewa uwargidarsa mahaifa ba tare da saninta ba

Lamarin ya jawo hankalin jami'an ‘yan sanda na yankin Owa-Oyibu tare da kungiyar ‘yan banga masu yaki da harkokin tsafi da ke shiyar.

“Baturen yan sanda na yankin ya kirawo a wayar sadarwa, inda ya sanar da mu rahoton faruwar rikicin, wanda kuma mun yi kokarin dakile cigabansa cikin gaggawa". Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Delta Muhammad Mustapha ya shaida.

Amma wani daga cikin jami'an rundunar yaki da masu aiyukan kungiyar asiri a yankin wanda ya bukaci da a sakaye sunansa, ya bayyana cewa kungiyoyin asirin sun shirya tsaf domin tunkarar dukkanin wani mataki da hukumomi za su dauka a kansu.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel