Oshiomhole ya sako wani tsohon gwamnan PDP a gaba a kan lallai sai ya shiga APC

Oshiomhole ya sako wani tsohon gwamnan PDP a gaba a kan lallai sai ya shiga APC

- Jam’iyyar APC na cigaba da kokarin ganin ta mamaye yankin kudu maso kudu da jam’iyyar PDP ke da karfi da yawan mabiya

- A kokarinta na son ganin ta wannan buri, PDP na yin dukkan iyawar ta domin ganin jawo tsohon gwamnan jihar Delta, Mista Emmanuel Uduaghan, zuwa cikinta

- Jam’iyyar ta APC ta dade tana kira ga tsohon gwamna Uduaghan a kan fita daga jam’iyyar PDP

A kokarinta na son ganin ta kwace karfi da yawan mabiya da jam’iyyar adawa ta PDP ke da shi a yankin kudu maso kudu, jam’iyyar APC mai mulki na yin dukkan iyawar ta domin ganin ta jawo tsohon gwamnan jihar Delta, Ummanuel Uduaghan, zuwa cikinta.

Oshiomhole ya sako wani tsohon gwamnan PDP a gaba a kan lallai sai ya shiga APC

Oshiomhole da Uduaghan

Kamar yadda tayi nasarar jawo tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio, zuwa cikinta, APC na son ganin Uduaghan ya dawo cikinta a jihar Delta domin samun damar kafa gwamnati a jihar cikin sauki kamar yadda take ganin zata yi a jihar Akwa Ibom.

DUBA WANNAN: Hukumar 'yan sanda tayi karin haske a kan rahoton birkice gidan tsohon gwamnan PDP

Jaridar Vanguard ta rawaito cewar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshimhole, ne a sahun gaba wajen matasawa tsohon gwamna Uduaghan ya bar PDP. Wasu na ganin hakan na da alaka da kyakykyawar alaka dake tsakanin mutanen biyu tun lokacin suna gwamnoni.

Sai dai duk da matsin lambar da yake fuskanta da kuma son ganin ya koma APC din, Uduaghan ya bayyana cewar tsohon gwamnan jihar, James Ibori, na rokonsa ya cigaba da zama a jam'iyyar PDP.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel